✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa da ’yarta sun lashe gasar gudun famfalaƙi a Kaduna 

Dattijuwa Elizabeth Nuhu Bawa ce ta zama Gwarzuwa a yayin da ’yarta, Grace, ta zo ta biyu a gasar tseren yada-ƙanin-wani

Wata dattijuwa da ’yarta mai shekara 17 sun lashe gasar tseren yada-ƙanin-wani a bikin raya al’adun al’ummar Kudancin Jihar Kada (SKFEST) ta bana.

Dattijuwa Elizabeth Nuhu Bawa ce ta zama Gwarzuwa a yayin da ’yarta, Grace, ta zo ta biyu a gasar.

’Yan tsere da dama ne suka kwashinsu a hannun dattijuwa Elizabeth da ’yarta Garda a gasar fa aka fafata a filin wasa na garin Kafanchan.

Grace mai shakara 17 ta ce ta so a ce ta doke mahaifiyarta domin ta zo ta ɗaya amma mahaifiyar ta fi ta kuzari.

Amma duk da haka ta ce tana fatan nan gaba za ta ba ta mamaki.