Wata dattijuwa da ’yarta mai shekara 17 sun lashe gasar tseren yada-ƙanin-wani a bikin raya al’adun al’ummar Kudancin Jihar Kada (SKFEST) ta bana.
Dattijuwa Elizabeth Nuhu Bawa ce ta zama Gwarzuwa a yayin da ’yarta, Grace, ta zo ta biyu a gasar.
’Yan tsere da dama ne suka kwashinsu a hannun dattijuwa Elizabeth da ’yarta Garda a gasar fa aka fafata a filin wasa na garin Kafanchan.
Grace mai shakara 17 ta ce ta so a ce ta doke mahaifiyarta domin ta zo ta ɗaya amma mahaifiyar ta fi ta kuzari.
Amma duk da haka ta ce tana fatan nan gaba za ta ba ta mamaki.