Shahararren dan tseren duniya dan asalin Jamaika Usain Bolt ya fafata da motar safa a Ajantina kimanin makwanni biyu da suka wuce.
dan tseren ya kai ziyara Ajantina ne a wani hutu da ya dauka don horar da matasa harkar tsere a wata cibiyar horar da matasa harkar tsere a wani kauye da ake kira Los Piletone da ke kusa da babban birnin Ajantina watau Buenos Aires.
An ce dan tseren ya yanke shawarar fafatawa da motar bas din ce don ya gwada bajintarsa a fagen tsere. Nan take jama’a suka kewaye filin don ganin yadda za ta kaya inda direban ya tuka tare da wasu fasinja a ciki yayin da Usain Bolt kuma ya takarkare da gudu don ganin ya wuce motar.
Sai dai direban ya daga wa Bolt kafa inda ya rika tafiya sannu a hankali al’amarin da ya sa Bolt ya wuce motar da wasu dakika.
Nan take jama’ar da ke wurin suka jinjinawa Bolt kuma suka yi masa fatan samun nasara a wasannin tseren da zai yi nan gaba.
Tuni Usain Bolt ya bayyana aniyarsa ta lashe lambobin zinare a gasar Olamfik ta 2016.
Usain Bolt ya fafata da motar safa
Shahararren dan tseren duniya dan asalin Jamaika Usain Bolt ya fafata da motar safa a Ajantina kimanin makwanni biyu da suka wuce.dan tseren ya kai…
