✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

United za ta kece raini da City a Old Trafford

Guardiola ya ce a yanzu Man United na cikin ganiyarta.

A ranar Asabar ce Manchester United za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan da ake hasashen zai yi zafi wanda kuma za a kalla a ko’ina a fadin duniya.

United ta yi nasara a wasanni takwas a jere kuma za ta iya kai wa ga mafi dadewa a gasar tun bayan da Alex Ferguson ya yi ritaya a matsayin koci a 2013.

City da ke mataki na biyu da maki hudu a saman United ta sha kashi a hannun Southampton a gasar cin Kofin Carabao a ranar Laraba.

Kocin City Pep Guardiola ya ce a yanzu Man United na cikin ganiyarta wanda hakan a bayyane yake.

United na dab da daukar aron dan wasan Burnley Wout Weghorst amma ba zai iya buga wasa ba saboda yana bukatar a yi masa rijista da a wannan Juma’ar.

Sai dai da wuya Anthony Martial ya buga wasan saboda raunin da ya ji a kafarsa, don haka Marcus Rashford, wanda ya ci kwallaye bakwai a wasanni shida da suka wuce, zai iya bugawa a matsayin lamba tara.