Manchester United na shirin fara tattauna batun sabon kwantiragi da dan wasan gabanta Marcus Rashford gabanin karshen wannan kaka.
United ta biijiro da zabin Karin shekara guda a kwantiragin Rashford, wanda zai sa ya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024, amma kuma sun kagara su cimma yarjejeniya ta tsawon lokaci.
- Ku zo mu hada kai don ciyar da Gombe gaba – Gwamna ga ’yan adawa
- Wahalar man fetur ta fara raguwa a Kano
Wasu majiyoyi sun ce United za ta so ta cimma yarjejeniya da Rashford a karshen wannan shekarar, ko kuma a farkon kaka mai zuwa.
Paris Saint Germain ta Faransa ta nuna sha’awar daukar Rashaford a baya, amma ana sa ran dan wasan mai shekaru 25 ya ci gaba da zama a United, inda yake kan ganiyarsa a karkashin mai horarwa Erik Ten Hag.
United na neman dan wasan gaba kafin kaka mai zuwa, sai dai Rashaford yana cikin tsarin mai horarwa, Ten Hag.