Akalla mutum 500,000 da rikicin yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya shafa za su amfana da kudi Fam miliyan 40 na ayyukan jinkai a jihohin Yobe da Borno.
Mukaddashin Shugaban Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Maiduguri, Dokta Clement Adams ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Damaturu yayin kaddamar da shirin jinkan don tallafa wa al’ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 14,500 a shekara 4 A Afirka –ECOWAS
- An rantsar da shugaban rikon kasar Sri Lanka
Ya bayyana cewa an samar da shirin ne da nufin tallafa wa marasa galihu ta hanyar kyautata rayuwarsu da bunkasa zaman lafiya da ilimi da lafiya da samar da abinci mai gina jiki da sauransu.
Jami’in ya ce, “Shirin zai gudanar da ayyukan jinkai a yankin kananan hukumomin jahar Bade a Jihar Yobe da kuma Shani a Jihar Borno, wanda zai shafin fannoni daban-daban.
“Zai karfafa tsare-tsaren shugabanci don bunkasa zamantakewa tsakanin al’umma da agaza wa harkokin gwamnati,” inji shi.
Kazalika ya ce, “Sabon shirin zai maida hankali wajen wanzar da zaman lafiya da karfafa wa harkokin shugabanci da zamantakewa, farfado da muhimman ababen more rayuwa da ayyukan ceton rayuwa da za su shafi mutum 156,888 kai-tsaye da kuma wasu mutum 362,307 a tsakanin kananan hukumomin biyu.”
Shugaban WFP a Damaturu, Dokta Agbessi Amewoa ya ce, wannan aiki daya ne daga cikin ayyukan da WFP ke aiwatarwa a tsakanikanin kananan hukumomi 17 da jihar ke da su.