✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UNICEF ta yi alkawarin taimakawa ilimin ‘ya’ya mata a Gombe

Babban jami’in Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya,  UNICEF da ke kula da ofishin su na shiyyar Bauchi Mista Phanu Pathak, ya…

Babban jami’in Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya,  UNICEF da ke kula da ofishin su na shiyyar Bauchi Mista Phanu Pathak, ya ce muhimmancin ilimin ‘ya’ya ya wuce kawai asa yara makaranta. Mista Phanu Pathak, ya bayyana hakan ne a Gombe a lokacin taron nazartar aikace-aikacen asusun Hukumar na jihohin Bauchi da Taraba da Adamawa da kuma Filato da suka gudanar a Gombe.

Ya kara da cewa, ilimin ‘ya’ya mata ba kawai sanya su makaranta shi ne ya wadatar ba, a tabbatar da cewa su kansu matan suna cikin lafiya, sannan kuma a tabbatar da sun kammala karatun su a dukkan matakin ilimi dan samun ingantacciyar rayuwa. Pathak, ya kara da cewa taron dubi da suke yi na tsakiyar shekarar 2019 da 2020 dan shirya tsarin tafiyar da samarwa da yara muhalli ne na musamman dan inganta rayuwar su.

Ya kuma hori gwamnati kan ta inganta harkar ilimi saboda yara su samu ilimi mai nagarta dan kara rage yawan yaran da basa zuwa Makaranta a jihohi wanda yanzu ake da kimanin yara dubu 600 a jihar Gombe. Sanann ya kuma ce, don samun mafita sai ma’aikatan sashin ilimi suna kaiwa Gwamnonin jihohin su da Kwamishinonin ilimi ziyara suna wayar musu da kai kan wasu muhimman al’amura da suka shafi ilimi. Daga nan sai ya ce hukumar UNICEF tana kara taimakawa ilimin yara da masu fama da karancin abinci mai gina jiki, saboda idan yaran suna makaranta za’a samu raguwar safarar yara da bautar da su da ake yi a duniya.