✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara

Wannan matsala ta nuna ƙarara yadda rayuwar yara ƙanana ke cikin haɗari da ƙarancin kotuna da kuma gidajen tsare ƙananan yara.

Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya.

A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai dubban ƙananan yara da gwamnati ta rufe su ba kuma tare da cikakken bayani ga iyalansu ba, wasu ma a yanzu babu cikakken bayani kan inda suke ko kuma halin da suke ciki.

Asusun ya ce a Nijeriya rufe ƙananan yara tare da yi musu shari’a ta zalunci ba bisa ƙa’ida ba na ƙara zama ruwan dare matakin da ke jefa yara cikin fargaba.

Rahoton ya ce wannan matsala ta nuna ƙarara yadda rayuwar yara ƙanana ke cikin haɗari da kuma yadda ake da ƙarancin kotuna da kuma gidajen tsare ƙananan yara.

UNICEF ɗin ya ƙara da cewa ana gwamutsa yaran a gidajen yari da manyan masu laifi sakamakon ƙananan laifuka da suka aikata abinda ke gurɓata tunaninsu a lokuta da dama kuma suke koyon wasu laifukan masu girma.

Rahoton ya ci gaba da cewa a bayanan da ya tattara a tsakanin shekarar 2018 da 2022 sama da mutane 87 ne ake tsare da su a gidajen yari haka siddan ba tare da sanin makomarsu ba, sai kuma ƙananan yara 1,279 da ake tsare da su wasu ma ba’a san inda suke ba.

Asusun ya gano cewa mafi yawan waɗannan mutane sun shafe sama da shekaru 5 a gidajen yarin, ba tare da an yanke musu hukunci ba.