✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UNESCO na son a bunkasa Tafkin Chadi don kyautata zaman lafiya

Hukumar Bunkasa Ilmin Kimiyya da Al’adu ta Majalisar dinkin Duniya (UNESCO) ta yi kira da a bunkasa tare da kirkiro hanyoyin sarrafa albarkatun tafkin kan…

Hukumar Bunkasa Ilmin Kimiyya da Al’adu ta Majalisar dinkin Duniya (UNESCO) ta yi kira da a bunkasa tare da kirkiro hanyoyin sarrafa albarkatun tafkin kan iyakokin kasashe na Chadi wadda ya hada Najeriya da Kamaru da Nijar da Afirka ta Tsakiya da kuma Chadi.  

Wannan kira ya fito ne daga bakin Mataimakin Babbar Daraktan bangaren Kimiyyar karkashin kasa na (UNESCO), Madam Flabia Schlegel, a yayin gudanar da taron MAB karo na biyar a Ibadan ta Najeriya.

Madam Schlegel ta ce akwai bukatar kasa da yanki da kuma duniya baki daya su hada karfi wajen maida wannan tafki na Chadi abin alfahari saboda kasancewarsa mabubbugar samun arziki wanda rayuwar kimanin mutane sama da miliyan 30 za ta iya dogaro a kansa. Amma abin takaici tafkin na dabaibaye  ne da tulin matsalolin da suka sha karfinsa, ciki  har da rashin zaba isasshen jari, rashin tsaro, amfani da tafkin fiye da kima, canjin yanayi da sauran su, wadanda suka hadu suka hana samun amfani ga miliyoyin mutane.

“A Watan Mayun wannan shekarar ce Hukumar Inganta Tafkin Chadin don amfanin al’ummar kasashen Kamaru, Nijar, Najeriya, Afirka ta Tsakiya da kuma Chadi ta bukaci taimakon UNESCO wajen cimma nasarorin dake tattare da ayyukan inganta harkokin tafkin wadda aka yi wa lakabi da BIOPALT.”

Babbar jami’ar ta kara da cewa, “Wannan shiri na BIOPALT yana da manufa wajen tunkarar dukkan kalubalen da ke tattare da tafkin, sannan ta yi kira ga dukkan kasashen da su hada hannu waje guda daya wajen  kirkiro wannan babbar farfajiyar da duniya za ta yi alfahari da ita. Wannan kuma wani abu ne da zai taka rawa wajen sake wanzar da zaman lafiya da jin dadin jama’a a yankin baki daya.” 

A karshe ta ce bisa hadin gwiwar dukkan kasashe da al’ummomin da nasarar ta shafa, UNESCO za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da  an samu damar cimma wannan buri cikin kankanen lokaci.