Dandalin sada zumunta na Twitter, ya ce zai toshe shafuka sama da 300 na gwamnatin Rasha, ciki har da na shugaban kasar, Vladimir Putin.
Twitter dai na zargin shafukan da yada labaran karya kan yakin Ukraine, sai dai kuma tun bayan mamayar kasar da Rasha ta yi, aka takaita ayyukan Twitter a Rasha.
- ICC za ta fara sauraron shari’ar aikata laifukan yaki a Sudan
- Duk jam’iyyar da ta karya Dokar Zabe za mu hana ta zabe a 2023 —INEC
Kamfanin, ya ce zai dauki mataki kan duk wata kasa da ta takaita amfani da Intanet yayin da take fagen yaki.
Rasha dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba tun bayan da ta mamayi Ukraine, kan abin da kasashe, musamman na Turawan Yamma ke ganin rashin dacewarsa.
Hakan ya sa aka dinga kakaba wa Rasha takunkumai daban-daban a wani mataki na hukuntata, sai dai kunnenta bisa alama har yanzu ya ki yin laushi game da yakin, duk da neman zaman sulhu da Ukraine din ke yi da ita.
Yakin ya yi sanadin salwantar rayukan dimbin mutane, kama daga kan dakarun soji da fararen hula a tsakanin kasashen biyu.