✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ukraine ta kashe sojojin Rasha 100 a Kherson

Ukraine ta ce ta tarwatsa wa Rasha rumbun makamai tare kashe sojoji akalla 100 da kuma lalata tankunan yaki

Ukraine ta yi ikirarin hallaka dakarun Rasha sama da guda 100 a wani kazamin fada a yankin Kherson da ke hannun dakarun na Rasha.

Rundunar tsaron Ukraine ta ce dakarunta sun yi nasarar tarwatsa wa Rasha ma’ajiyar makamanta tare kashe sojoji akalla 100 da kuma lalata tankunan yaki bakwai a Kherson a ranar Juma’a.

Ta kara da cewa sojojin Ukraine sun kuma katse layin dogo da ke kaiwa zuwa Kherson ta Kogin Dnieper.

Kawo yanzu dai dai ba a iya tantance gaskiyar ikirarin na Ukraine ba.

Amma katse layin dogon zai dakile sojojin Rasha da aka girke a Yammacin Kogin Dnieper daga samun makamai daga tsallaken Gabashin kogin.

Hukumomin tsaron Birtaniya dai na ganin lalata gadojin da ke kaiwa zuwa yankin Dnieper ya jefa sojojin Rasha da ke Yammacin Kogin Dnieper a cikin karin hadari.

A baya-bayan nan dai Ukraine tana amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da ta samu daga kasashen Yammacin duniya wajen kai hare-hare a Kherson.

Yankin shi ne na farko a fadin Ukraine da dakarun Rasha suka kwace tun bayan kaddamar da mamayarsu a watan Fabrairu.