Kasashen Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunoni na ba-zata kuma mafi girma tun bayan barkewar yaki a tsakaninsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ta rawaito cewa, kasashen biyu sun yi musayar fursunonin ne a ranar Laraba wanda ya shafi kusan mutum 300.
- An zabi Tambuwal a matsayin sabon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya
- DSS ta bukaci ASUU ta janye yajin aikinta
Musayar ta hada da wasu ’yan kasashen waje 10 da kuma kwamandojin da suka jagoranci bai wa Ukraine kariya a Mariupol a farkon wannan shekara.
Daga cikin ’yan ketaren da aka saka din sun hada da ’yan Birtaniya biyu da wani dan kasar Moroko wadanda aka yanke wa hukuncin kisa tun a watan Yuni bayan da aka kama su suna taya Ukraine yaki.
Kazalika, musayar ta hada da wasu Amurkawa biyu, ’yan Birtaniya uku da kuma wani dan Croatian da kuma wani dan Switzerland.
Sai dai kuma lamarin musayar ya ba da mamaki ainun duba da ko a ranar da aka yi musayar sai da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ba da sanarwar hada kan wasu dakaru don ci gaba da gwabzawa.