✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UEFA ta kutsa sunan Ronaldo cikin tawagar 2019

Duk da tauraron dan wasa Cristiano Ronaldo bai samu kuri’a ba, Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai UEFA ta sauya jerin ‘yan wasan tawagarta na…

Duk da tauraron dan wasa Cristiano Ronaldo bai samu kuri’a ba, Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai UEFA ta sauya jerin ‘yan wasan tawagarta na shekara ‘yan sa’o’i kafin sanar da ita saboda babu Cristiano Ronaldo a ciki.

Jaridar Daily Mail ta kasar Ingila ta ruwaito cewa, magoya bayan kwallon kafa a Nahiyar Turai ba su jefa wa Ronaldo kuri’u masu yawa ba, inda suka zabi Lionel Messi da Sadio Mane da kuma Robert Lewandowski a matsayin ‘yan wasan gaban tawagar. Hakan na nufin babu gurbin Ronaldo kenan.

A ranar Laraba ne dai Uefa ta sanar da tawagar, wadda aka saba fitarwa ta zakakuran ‘yan wasa 11 a duk shekara. Sai dai Male ta ce, dan wasan tsakiyar Chelsea kuma na Faransa wato Ngolo Kante aka cire, inda aka maye gurbinsa da Ronaldo.

Hatta tsayuwar ‘yan wasan wato formation ta sauya a wannan karon kasancewar akwai ‘yan gaba hudu a tawagar sabanin uku da aka saba. Akan yi tsarin 4-3-3 a tsawon shekara biyar in banda 2017 da aka zabi 4-4-2, in ji Male.

Jaridar ta kara da cewa, dalilin yin hakan shi ne saboda Ronaldo na hudu ya yi a kuri’un da aka kada wa ‘yan wasan gaba – a bayan Messi da Lewandowski da Mane – kuma tun a makon da ya gabata Uefa ta so fitar sunayen ‘yan tawagar amma abu ya ci tura saboda babu Ronaldo a ciki.

Mahukunta ba su ji dadin lamarin ba kuma hakan ne ya sa aka sauya tsayuwar ‘yan wasan bayan cire dan tsakiya guda daya, wanda aka ce Ngolo Kante ne.

Mai magana da yawun Uefa ya bayyana cewa, an yanke hukuncin shigar da Ronaldo ne saboda lashe gasar Nations League da kasarsa Portugal ta yi. “An zabi tawagar ta bana ne ta hanyar bai wa magoya baya zabinsu ba kawai saboda kokarin da ‘yan wasa suka yi ba ne,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Saboda haka, akwai ‘yan wasan da suka lashe Champions League guda biyar da kuma wadanda suka je wasan karshe a Nations League (da Ronaldo wanda ya ci kofin). Tsayuwar kan canza a lokuta kuma hakan ba sabon abu ba ne.”

Tawagar Uefa ta 2019

Mai tsaron raga: Alisson Becker

‘Yan baya: Alexander-Arnold, De Light, Van Dijk, Robertson

‘Yan tsakiya: De Jong, De Bruyne

Yan gaba: Messi, Lewandowski, Ronaldo, Mane