Hukumar Kwallon Kafa ta Tarayyar Turai (UEFA) ta dakatar da kungiyoyin kasar Rasha daga gasar Kofin Zakarun Turai (Champions League) ta kakar badi.
UEFA ta fitar da hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
- Tayar jirgin saman Dana ta kama da wuta a Fatakwal
- Mun yi Sallah cikin kunci saboda rashin albashi – Ma’aikatan Kano
“Ba za mu bar kungiyoyin kwallon kafar Rasha su fafata a kakar wanni ta 2022/2023,” kamar yadda hukumar ta sanar.
Tun a watan Fabrairu ne dai aka dakatar da kungiyoyin kasar guda uku ana tsaka da ci gaba da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.
Kazalika, hukumar ta dakatar da kungiyoyin mata daga shiga gasar da za a yi a watan Yuli a kasar Ingila.
Kasar Portugal dai wacce ta yi rashin nasara a fafatawarta da Rashar a wasan neman cancantar shiga cin kofin duniya a yanzu ita ce za ta maye gurbin Rashar a rukunin C da sauran kasashe kamar Netherlands da Sweden da kuma Switzerland.
UEFA ta kuma ce kungiyar ba ta cancanci neman buga gasar cin kofin zakarun Turai a shekarar 2028 ko 2032 ba, saboda mamayar Ukraine din.
Daga bisani dai Hukumar Kwallon Kafar Rasha ta daukaka kara kan matakin a kotun wasanni kan dakatarwar, kafin ta janye karar a watan da ya gabata.
Matakin na UEFA dai ya kuma shafi cire kasar daga cancanta da buga gasar ’yan kasa da shekara 21 a gasar Turai. (AFP)