’Yan sanda sun kama wani magidanci da ya sayar da ’ya’yansa biyar a kan kudin da bai kai Naira miliyan 1.2 ba a Jihar Sakkwato.
Dubun mutumin ta cika ne bayan da aka gano karin kananan yara 21 da wata ‘yar sanda mai safarar yara da kawarta suka sato daga Jihar Sakkwato suka kai su Abuja.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Hayatu Kaigama, ya ce bayyana cewa bincike ya gano cewa magidancin, mazaunin unguwar Tudun Wada, ya sayar da kananan yara 28 ga wata ’yar sanda mai suna ASP Kulu Dogonyaro da abokiyarta Elizabeth.
Da yake holen wadanda ake zargin, kwamishinan ya bayyana cewa a cikin yaran da mutumin da ya sayar har da ’ya’yan cikinsa biyar, inda su ASP Kulu Dogonyaro suka biya shi tsakanin N150,000 zuwa N150,000 a kan kowane yaro.
- Majalisar Dattawa ta amince a ninka albashin ma’aikatan shari’a sau uku
- NAJERIYA A YAU: Mafi Karancin Albashi: Shin Me Ma’aikata Ke Fatan Samu?
Kwamishinan ya ce zuwa yanzu rundunar ta gano tare da ceto wasu yara 21 da barayin suka sato daga jihohi daban-daban.
Ya bayyana cewa barayin yaran suka yi safarar yaran ne ta hanyar yin sojan gona da cewa za su sama musu kyakkyawar kula a hannun kungiyoyi masu zaman kansu.
Aminiya ta ruwaito a watan Mayu yadda aka kama wata hafsar ’yan sanda da wata mai taimaka mata suka sato kananan yara biyar, ciki har da wata jaririya ’yar mako biyu a duniya daga Jihar Sakkwato za su kawo su Abuja.
Sauran fasinjojin motar da ke hanyar Abuja sun fara zargin ASP Kulu Dogonyaro da abokiyarta, sun sato yaran ne bayan sun lura da yadda suke musguna wa yaran.
Da zuwansu Abuja kafin a je tasha, direban da sauran fasinjojin suka wuce da su kai-tsaye zuwa ofishin ’yan sanda da ke Dei Dei, kafin a karasa Kubwa, inda su ASP Kulu Dogonyaro za su sauka.
Yanzu haka an tisa keyar Kulu da abokiyarta Elizabeth zuwa Jihar Sakkwato inda ake ci gaba da bincike.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta yi holen su Kulu da abokin harkarsu mai suna Bala Abubakar da ke unguwar Tudun Wada.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Hayatu Kaigama, ya ce zuwa yanzu rundunar ta gano tare da ceto wasu yara 21 da barayin suka sato.