Dan takarar gwamnan Jihar Kaduna na jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani, ya zabi Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takararsa a babban zaben 2023 da ke tafe.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Sanatan Kaduna ta Tsakiya, ya ce ya zabi Hadiza Balarabe a matsayin abokiyar takararsa bayan kammala tuntube da neman shawarwarin masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, Dokta Hadiza Balarabe wadda ke zaman mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna, ta bayar da gudunmuwa mai tarin yawa a nasarorin da gwamnatin Kaduna ta samu karkashin jagorancin Gwamna Mallam Nasir El-Rufai musamman a fagen samar da ababen more rayuwa da inganta ci gaban al’umma.
“Ina mai farin cikin sanar da cewa na zabi mai girma Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarata a zaben gwamnan Jihar Kaduna na 2023.
“Dokta Hadiza Balarabe ta ba da gudunmawa sosai a gagarumin ci gaban da gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta kawo a fannin samar da ababen more rayuwa da kuma ci gaban jama’a.
“Dokta Balarabe ta nuna kwazo da hadin kai wajen sauke nauyin da aka dora mata a matsayin Mataimakiyar Gwamna, wanda haka ya kara mata daraja hatta a idon masu adawa da ita a jihar.
“A daidai wannan gaba ce nake kira ga al’ummar Jihar Kaduna da su goyi bayan zabin Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarata.
“Ina kuma shawartarsu da su fito su kada kuri’ar zaben tikitinmu a babban zaben 2023 mai zuwa, wanda hakan ne zai ba mu damar inganta ci gaban Jihar Kaduna.
“Mun kudiri aniyar ganin Jihar Kaduna ta zama abar kwatance da kuma abun koyi ta fuskar jagoranci nagari,” a cewar sanarwar.