✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UAE Ta Tsaurara Wa ‘Yan Najeriya Matakan Shiga Kasarta

Yanzu dole sai mutum ya nuna karfin nauyin aljhunsa da takamaimai inda zai sauka da kuma tikitin jirginsa na dawowa

Haddiyar Daular Larabawa (UAE) ta gindaya wasu sabbin sharuddan masu tsauri ga ’yan Najeriya masu son zuwa Dubai.

Aminiya ta gano sharuddan da UAE ta sabinta a shafin neman izinin shiga kasarta, sun shafi ’yan Najeriya ne kadai, kuma dole ne mai son shiga kasar ya cika su kafin a ba shi biza.

Daga cikin sharuddan wajibi ne dan Najeriya ya bayar da cikakken bayani da adireshin masaukinsa a UAE, otel ne ko wanninsa.

Sai bayanin ajiyar bankin mutum da abin da ke ciki, da hada-hadar da ya yi na tsawon wata shida.

Zai kuma gabatar da tikitin jirgin sama na dawowa gida da zarar wa’adin zamansa a can ya kare.

Wadannan sharudda sun tayar da hankalin ’yan Najeriya masu son zuwa UAE domin kusuwanci ko yawon bude ido, a yayin da suke ta kokarin cika su.

Kafin wadannan sharudda ’yan Najeriya na samun damar shiga da fita daga kasar cikin sauki a duk lokacin da suke so.

A shekara ana samun ’yan Najeriya 200,000 da ke zuwa Dubai domin kasuwanci ko yawon bude ido.

Rahotanni na cewa, wannan mataki ba zai rasa nasaba da bidiyon wasu matasa da ake zargin ’yan Najeriya ne, suka yi ta yawo da makami suna tayar da hankalin jama’a tare yin fashe-fashe.