✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya ta tsare ’yan leken asirin Isra’ila 33 a Istanbul

Turkiyya ta tsare wasu mutane 33 bisa zargin shirin sace mutane da kuma yin leken asiri a madadin hukumar leken asirin Isra'ila.

Turkiyya ta tsare wasu mutane 33 bisa zargin shirin yin garkuwa da mutane da kuma yin leken asiri a madadin hukumar leken asirin Isra’ila ta Mossad.

Ministan harkokin cikin gida Ali Yerlikaya ya sanar cewa an kama wadanda ake zargin ne a samamen da jami’an tsaro suka kai a wasu larduna takwas na birnin Istanbul da kewaye.

A ranar Talata ofishin ministan ya fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda jami’an tsaro dauke da makamai suna fasa kofofin gidajen wadanda ake zargin sannan suka buga musu ankwa.

Yerlikaya ya ce, “Ba za mu taba bari a rika gudanar da ayyukan leken asiri a kan hadin kan kasa da hadin kan kasarmu ba.” 

Ofishin mai shigar da kara na Turkiyya ya ce akwai wasu karin mutane 13 da ake nema bisa zargin, da suka tsere.

Har yanzu dai ba a bayyana ko wadanda da ake zargin Isra’ilawa  ba ne, ko kuma Turkawa ne da ke aiki da Mossad.

Dangantaka tsakanin Turkiyya da Isra’ila ta yi tsami ne bayan barkewar yakin Isra’ila da Hamas a watan Oktoban 2023.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya zama kan gaban cikin manyan masu sukar firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a duniya.

A makon jiya, Erdogan ya kwatanta Netanyahu da Adolf Hitler, ya kuma bukaci kawayen Isra’ila na yammacin Turai su janye goyon bayansu ga “ta’addanci” da sojojin Isra’ila suke aikatawa a Gaza.

Har ila yau, Erdogan ya janye jakadan Turkiyya a Tel Aviv, ya kuma dage wajen ganin an gurfanar da kwamandoji da shugabannin siyasan Isra’ila a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da ke birnin Hague.

Jam’iyyarsa ta AKP ta kuma jagoranci dubban masu zanga-zanga a birnin Istanbul domin nuna adawa da Isra’ila.