✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya ta kaddamar da hari a kan ’yan tawayen Kurdawa

An girke jami'an tsaro 1,600 domin fatattakan mayakan Kurdawa a Kudancin Turkiyya.

Gwamnatin Turkiyya ta kaddamar da sabon farmaki da nufin murkushe ’yan awaren Kurdawa masu dauke da makami a Kudancin kasar da ke iyaka da Syria.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Turkiyya ta ce dakaru 1,600 da suka kunshi sojoji da ’yan sanda da ’yan sa kai na kauya aka hada su a cikin tawaga 96 domin fatattakar ’yan awaren.

Kamfanin dillancin labaru na Andalou ya ce za a yi aikin na Operation Eren-8 Amanoslar na yankunan Osmaniye, Hatay da kuma Gaziantep  masu iyaka da Kudu maso Yammacin Syria.

Wannan kari ne a kan ayyukan soji guda bakwai na yaki da ta’addancin da gwamnatin kasar ta kaddamar a kan mayakan Kurdawa a yankin Gabashin kasar da Kurdawa ne mafiya rinjaye.

Sama da shekara 40 ke nan gwamnatin kasar ke yakar Kurdawa bisa zargin ta’addanci, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

Kimanin kashi 15% na al’ummar kasar Turkiyya ne Kurdawa wanda gwamnatin kasar ba ta yin wata-wata wajen dakile duk wani yunkurinsu na ballewa daga kasar.