Babban bankin kasar Turkiyya a ranar Juma’a ya bayar da sanarwar haramta amfani da kudaden internet na cryptocurrency da suka hada da bitcoin da ake amfani da su wurin yin cinikayya.
Babban bankin kasar ya ce, haramcin zai fara aiki daga ranar 30 ga Afrilu, 2021, saboda hadarin yin cinikayya da cryptocurrency.
- ’Yan sa-kai sun aika ’yan bindiga lahira a Kasuwar Dansadau
- An haifi jariri da azzakari uku
- Matawalle ya sauke basarake kan ba wa soja mai sayar da makamai sarauta
Haramcin ya shafi tura kudaden cryptocurrency don yin wata sayayya ko a matsayin ladan wata hidima ko aiki da aka yi.
Babban bankin ya ce hadarin dake tattare da sabgar ya hada da rashin ingantaccen tsarin sanya ido da kuma uwa-uba rashin dawo da kudaden da aka yi asara na bangarori biyun yayin mu’amalar kudaden, da ma yiyuwar yin amfani da su ta hanyar da bata dace ba.