✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote da BUA za su gurfana a majalisa kan badakalar haraji

Majalisar Wakilai na binciken kamfanonin BUA da Dangote cikin jerin kamfanoni da cibiyoyin gwamnati 113 kan badakalar kudaden haraji.

Majalisar Wakilai ta umarci kamfanonin BUA da Dangote su bayyana a gabanta don amsa tambayoyi kan zirarewar kudaden harajin Gwamnatin Tarayya.

Kamfanonin simintin BUA da Dangote na cikin jerin kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya 113 da za su amsa tambayoyi kan wannan lamari.

Shugaban kwamitin binciken kudaden jama’a na majalisar, Bamidele Salam, ya sanar cewa shugabannin kamfanonin ko manyan akantocinsu ne za su hallara domin amsa tambayoyin.

Bamidele Salam ya ce binciken zai mayar da hankali ne kan rashin biyan kudaden haraji ga gwamnati, rashin bin ka’idojin da doka ta shimfida wajen biya, da kuma zirarewar kudaden.

Ya ce binciken zai fara ne daga ranar 30 ga watan nan na Yuli zuwa 8 ga Agusta, 2024, kuma majalisar za ta yi tsattsuran hukunci kan duk kamfani ko cibiyar gwamnati da ta ki amsa gayyatar.

Sanarwar ta ce ana bukatar, “kamfanonin su zo da duk takardun da ake bukata.”

Bankunan First Bank, Zenith Bank, Guarantee Trust, Access Bank, Polaris, FCMB, Fidelity da Keystone na cikin masu amsa tambayoyin.

Hakazalika kamfanin hakar mai na Shell Develompent Company da kamfanin lemon kwalba 7Up da kamfanin mai na Durbi Oil.

Sauran kamfonin abinci irin su C-Way Food & Beverages da kamfanin madarar Fan Milk da kamfanin  Rite Food Ltd; Guinness Nigeria Plc;  Pabod Int’l Breweries; Champion Breweries; Agio Power Plant (Kwale Okpai Power Plant); Euro-Global and Disability Plc.

Hukumomi da cibiyoyin gwamnati da za a bincika sun hada da; Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci, wadda za a bincika kan zargin karkatar da kudaden tallafin COVID-19.

Hakazalika za a binciki Cibiyar Yaki da Yaɗuwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) kan zargin karkatar da kudaden yaki da cutar COVID-19.

Hukumar Gidan Radio ta Kasa (FRCN) kuma za ta amsa tambayoyi kan zirarewar kudaden shiga ta kafar Remita.

Sai Majalisar Karamar Hukumar Gwagwalada da za ta amsa tambayoyi kan zargin almundhana da rahoton shekarar 2020 da ofishin babban mai binciken kudi na kasa ya bankado.

Sauran da ake zargi a rahoton sun hada da:

Ma’aikatar Tsaro, Matatar Mai ta Kaduna, Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa na kuma Hukumar Iskar Gas ta Kasa (NLNG) da Ma’aikatar Sufuri ta Kasa

Akwai kuma Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare, Jami’ar Sojoji da ke Jihar Borno, Ma’aikatar Ma’adinai, Hukumar Kogin Neja Delta, Ma’aikatar harkokin waje, Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO).

Hakazalika akwai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Kamfanin dDllanccin Labaran Najeriya (NAN) da Hukumar Aikin Dan Sanda da Cibiyar Yaki da Cutar Kuturta da Tarin Fuka da Hukumar Kidaya ta Kasa da sauransu da suka hada jami’o’i da kwalejin ilimi da cibiyoyin lafiya da sauransu.