Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta soke tsarin biyan tallafin man fetur.
A wata hira da ya yi da kafar Bloomberg a ranar Litinin, Dangote wanda shi ne mamallakin matatar mai na Dangote, ya ce tallafin man fetur zai sa gwamnati ta “biyan kudaden da bai kamata ta biya ba,” don haka akwai bukatar a soke shi.
Ya nace cewa gwamnatin Bola Tinubu ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.
A yayin jawabinsa na karbar aiki a a ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaba Tinubu ya ayyana kawo karshen tallafin man fetur.
- Za a kai shugaban ’yan sanda kotu kan kudin otel N625m
- ’Yan bindiga sun kashe limami a masallaci a Abuja
- Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno
Amma cikin gaggawa ya maido da shi bayan da hauhawar farashin kayayyaki ya karu.
An dauki wani mataki na kawo karshensa a farkon watan Satumba lokacin da aka sassauta farashin man fetur, amma kuma sai ya kansace farashin ya gaza matakin kasuwa.
Amma Dangote ya ce: “Ina ganin lokaci ya yi da ya kamata a cire tallafin domin duk kasashe da ku kusa da mu sun soke shi.
“Farashin man fetur dinmu ya kai kusan kashi 60 na farashin kasashen da ke makwabtaka da mu kuma muna da iyaka da su, don haka ba ya dorewa.
“Gwamnati ba za ta iya biyan tallafin ba.”
Shawarar Dangote ta biyo bayan fara aikin dakon man fetur daga matatarsa a baya-bayan nan, da kuma karin farashin litar man zuwa N950 a jihar Legas, da kuma sama da N1000 a yankin Arewa.
A cewarsa, samar da man fetur daga matatarsa zai taimaka wajen rage matsin lamba a kan Naira, sannan kuma ya tabbatar da mallakar rijiyoyin mai guda biyu da ake sa ran za a samu a watan gobe.
Ya ce: “Tallafi lamari ne mai matukar muhimmanci. Da zarar ka ba da tallafin wani abu to mutane za su tsuga farashi sannan gwamnati za ta biya abin da bai kamata ta biya ba. Lokaci ya yi da za a kawar da tallafin.”