daya daga shahararrun aftocin fina-finan Indiya da suka samu nasara, kuma wadanda suka dade ana damawa da su, shi ne Deb Anand. Gaskiyar wannan batu karara take, musamman ma ga wadanda suka dade suna kallon fina-finansa.
A lokacin da wakilinmu ya lalabi kafar sadarwar intanet, domin samo tarihi da labarin fadi tashin Deb Anand, hakarsa ta cimma ruwa, inda ya samo ingantattun bayanai game da jarumin.
Shi dai Deb Anand, wanda aka fi saninsa da lakanin Debdutt, an haife shi ne a ranar 26 ga watan Satumba, na shekarar 1923 kuma ya rasu ne a ranar 3 ga Satumba, 2011. Ya yi rayuwarsa a titin 2nd Iris Park, Unguwar Juhu, da ke birnin Bombay na kasar Indiya. Mutum ne shi mai matsakaicin jiki, mai tsawon kafa biyar da inci bakwai.
Bayani ya gabata cewa, ba haka nan daga ruwa sai kuka ya shiga harkar fim ba, domin kuwa ya yi karatu mai zurfi a zamanance. Ya yi karatun digiri a fannin Adabin Ingilishi, wanda haka ya ba shi damar shiga rukunin aftoci masu ilimi da fasaha a harkar shirya fina-finai, a kasar Indiya.
An haifi Deb Anand ne a garin Gurdaspur da ke cikin tsohuwar Jihar Punjab. Sunan mahaifinsa, wanda lauya ne, Pishorimal Anand. Kuma an samu bayanin da ya nuna cewa, ya kamu da son shiga harkar fim ne tun yana dan makaranta, amma ya yi hakuri har sai da ya kammala digirinsa na farko, inda daga nan ya bar gida. Bayan ya bar garinsu, jarumin bai zame ko’ina ba sai birnin Mumbai, inda ya tafi da zimmar kutsa kansa cikin sana’ar fim.
Da ya isa birnin Mumbai, bai samu nasarar fadawa cikin harkar fim kai tsaye ba, sai da ya fara yin aiki na wucin gadi, a wata ma’aikata da ke kula da harkokin sojoji. A lokacin nan, an rika biyansa albashin Rufi 160 ne kacal a wata.
Fitaccen jarumi kuma mai shirya fim a Indiya, Ashok Kumar ne ya fara jaraba Deb Anand cikin fim, inda ya ba shi wani dan karamin gurbi a cikin fim din Ziddi. Fim din ya samu nasara sosai kuma ya ba Deb Anand damar fara sanin makamar harkar fim. Da ya ga cewa ya fara bude ido a harkar, bai bata lokaci ba, sai kawai ya bude kamfanin kashin kansa, domin shirya fina-finai. Sunan kamfanin nasa Nebketan, kuma a nan birnin Mumbai ya kafa shi.
Fim din da kamfanin nasa ya fara shiryawa da farko, shi ne fim din Baazi, wanda ke ba da labarin muggan masu aikata laifuffuka, kuma abokinsa, Guru Dutt ne ya ba da umurni a fim din. Fitaccen mai rubuta wakokin fina-finai, Sahir Ludhiabi ne ya rubuta fitacciyar wakar fim din, mai taken Tadbeer se bigdi huyee takdeer bana de. Wakar ta taimaka wa fim din ya samu karbuwa sosai, wanda haka ya sanya Deb Anand cikin sahun masu shirya fina-finai na gaba-gaba a kasar Indiya.
Bayan fitar wannan fim da samun nasararsa, sai kuma haka ta sanya fina-finai guda uku da suka biyo baya, su ma suka zama masu nasara. Wadannan fina-finai kuwa su ne Rahee da fim din Aandhiyan da kuma Tadi Driber.
A matsayinsa na afto kuwa, fim din da ya fara daga tutarsa, shi ne fim din Hum Ek Hain, inda ya fito da hazakarsa da kwarewarsa ta dan wasa. Tun daga nan aka shaida kokarinsa, musamman ma yadda ya kware wajen iya jera magana mai azanci cikin sauri. Haka kuma ya fitar da kansa, inda ya bambanta kansa da sauran aftoci, wato da yake fitowa da hulunan malfa iri daban-daban. Ya nuna irin wadannan fasahohin a fina-finansa na Munimji da fim din CID da kuma fim din Paying Guest.
Irin yadda ya nuna namijin kokari a matsayinsa na kwararren afto a cikin fim din Kala Paani, ya samar masa da kambi, a lokacin da ya ci kyautar Fiyayyen Afto, wanda Mujallar Filmfare ta ba shi. Haka ma, fim dinsa mai kala na farko da ya fara fitowa, mai suna Guide, wanda kuma wansa, bijay Anand ya ba da ummurni, shi ne ya samu kambin ingantaccen fim dinsa. Wannan kambi ko kyauta, Mujallar Filmfare din ce ta kara ba shi. Haka kuma, ya taba samun irin wannan kambi, a matsayinsa na fitaccen dan fim na tsawon rayuwa.
Baya ga kasancewarsa mai shirya fina-finai kuma afto mai fitowa cikin fina-finan Indiya, Deb Anand kuma ya jaraba zama darakta, mai ba da ummurni a wasu fina-finan. Shi ne ya ba da ummurni cikin fim din Hare Ram Hare Krishna. Ya fito ne tare da Zeenat Aman, inda shi ne ma fim dinta na farko. Wato shi ne ma ke nan ya fara gabatar da jarumar cikin fim. Ya fito cikin fim din ne a matsayin dan ci-rani, kuma ga shi kamar talasuru, mara karfi.
Deb Anand, ba ga sana’ar fim kadai rayuwarsa ta tsaya ba, domin kuwa ya jaraba shiga harkokin da suka jibanci siyasa. Yana daya daga cikin kalilan din ’yan fim a Indiya da suke saka kansu cikin harkokin siyasa, duk da cewa bai shiga wata takarar mukami ba, amma dai yana jagorantar ’yan fim wajen yaki da gwamnati, musamman ma idan ta fito da wani tsari ko doka da ke kawo wa al’umma barazana. Misali, akwai lokacin da ya taba jagorantar ’yan uwansa ’yan fim, inda suka kalubalanci wani shiri da Gwamnatin Firaminista Indira Ghandi ta fito da shi, wanda ya shafi al’ummar kasa baki daya, wanda kuma suka ga lallai zai iya kawo matsala ga al’umma. Haka kuma, mafi yawan fina-finan da yake shiryawa ko kuma yake fitowa a cikinsu, suna dauke da darussa masu yawa da suke nuna irin akidarsa ta fada da zalunci da kuma abubuwan da ke faruwa a duniya gaba daya, wadanda suka shafi zamantakewar al’umma.
Deb Anand ya yi aure, inda ya auri ’yar fim mai suna Kamini Kartik. Haka kuma ya dade yana soyayya da wata ’yar fim kuma mai wakar fina-finan Indiya, mai suna Suraiya.
A cikin watan Satumba na shekarar 2007 ne Firaministan Indiya, Dokta Manmohan Singh ya jagoranci kaddamar da littafin rayuwar Deb Anand. Littafin, wanda shi ya rubuta abinsa da kansa, wanda kuma yake cikin Ingilishi, sunansa Romacing with Life.
Haka kuma, Cibiyar Harkokin Kasuwanci Da Masana’antu Ta kasar Indiya (FICCI), ta zabi Deb Anand, ta karrama shi da kyautar fitaccen dan fim da ke raye, domin irin gagarumar gudunmowar da yake bayarwa ga harkokin nishadantarwa da al’amuran shakatawa a kasar Indiya.
Bayan wannan, shugaban kasar Indiya, ya ba shi kyautar da suke kira da sunan Kambin Padma Bhushan, wanda shi ne kambi mai daraja ta uku, cikin kyaututtukan karramawa da ake ba ’yan kasar Indiya da suka nuna kwazo a rayuwarsu.
Ga jerin fina-finan da Deb Anand ya fito a cikinsu: Mr. Prime Minister da Aman Ke Farishtey da Lobe at Times Skuare da Censor Main Solah Baras Ki da Return of Jewel Thief da Gangster. Sauran sun hada da Awwal Number da Kishen Kanhaiya da Lashkar da Sachche Ka Bol Bala da Hum Naujawan da Anand Aur Anand da Swami Dada da Man Pasand da Lootmaar.
Wasu fina-finan nasa kuma su ne: Des Pardes da Darling Darling da Chhupa Rustam da Heera Panna da Joshila da Shareef Budmaash da Yeh Gulistan Hamara da Gambler da Hare Raama Hare Krishna da Tere Mere Sapne da Johny Mera Naam. Haka kuma, wasu fina-finan sun hada da Prem Pujari da Mahal da Duniya da Jewel Thief da Pyar Mohabbat da Guide da Teen Debian da Sharabi da Hum Dono da Solba Saal da C.I.D.da Funtoosh da Tadi Driber da Rahi da Aandhiyan da Baazi da Do Sitare da Madhubala da Ziddi da Aage Badho da Mohan da kuma fim din Hum Ek Hain.
Tunawa da gwagwarmayar marigayi Deb Anand a fagen shirin fina-finan Indiya
daya daga shahararrun aftocin fina-finan Indiya da suka samu nasara, kuma wadanda suka dade ana damawa da su, shi ne Deb Anand. Gaskiyar wannan batu…