Manjo Janar Muhammadu Buhari mai ritaya shi ne mutum na biyu da ya mulki Najeriya a matsayin soja da kuma farar hula.
Haka kuma shi ne na biyu a daɗewa kan kujerar mulkin Najeriya.
Lokacin da ya yi mulkin soji ya yi aiki ba-sani ba-sabo musamman wurin yaƙi da cin hanci da rashawa inda ya yi ta ɗaure tsofaffin ƴan siyasa da ƴan kwangila.
Tuna Baya: Tarihin Shugaban kasar Najeriya Alhaji Shehu Shagari
Tuna Baya: Tarihin shugaban ƙasar Najeriya: Janar Olusegun Obasanjo
Sannnan ya tilasta wa kowa da kowa bin doka ƙarƙashin shirinsa na Yaƙi da Rashin Ɗa’a.
Bayan shekara guda soji suka yi masa juyin mulki, abin da ya sa ake ta ganin da an ba shi dama da Najeriya ta cigaba.
Don haka lokacin da mulki ya koma hannun farar hula a 1999 ƴan Arewa suke ta fatan Allah Ya dawo da shi kan mulki.
Tun da ya amince ya karɓi kiran al’umma ya tsaya takara ba a samu wani mai farin jinin siyasa a Arewacin Najeriya kamarsa ba.
Tuna Baya: Tarihin Shugaban Mulkin Sojin Najeriya Janar Murtala Muhammad
Tuna Baya: Tarihin Shugaban Mulkin Sojin Najeriya Janar Yakubu Gowon
Sai dai sau uku yana ta faɗuwa a zaɓe daga 2003 zuwa 2011.
Sai a zaɓen 2015 ya yi nasarar cin zaɓe kuma ya yi tazarce a 2019.
Amma fa duk burin da mutane suka ci akan mulkinsa babu wanda ya samu.
Domin kuwa an shiga ƙuncin rayuwa, da matsin tattalin arziki, da ƙaruwar rashin tsaro da cin hanci da rashawa.
Kuma da yake sai a shekarar 2023 ɗin nan ne ya kammala mulkinsa kawo yanzu lokaci bai yi ba da za a iya tantance dalilan da suka sa ya yi faɗuwar baƙar tasa a idon al’umma.