✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tuna Baya: Tarihin Shugaban Mulkin Sojin Najeriya Janar Murtala Muhammad

Janar Murtala Ramat Muhammad, sojan nan da hotonsa ke jikin Naira Ashirin shi ne shugaban ƙasar Najeriya na huɗu bayan samun ƴancin kai. Watanninsa shida…

Janar Murtala Ramat Muhammad, sojan nan da hotonsa ke jikin Naira Ashirin shi ne shugaban ƙasar Najeriya na huɗu bayan samun ƴancin kai.

Watanninsa shida kacal ya yi a kan mulki amma ayyukan da ya yi sun sa ba za a taɓa mantawa da shi a tarihi ba.

Shi ne ya jagoranci mayar da dimokradiyyar Najeriya tsarin shugaba mai cikakken iko irin na Amurka saɓanin tsarin firaminista irin na Burtaniya.

Tuna Baya: Tarihin Shugaban Mulkin Sojin Najeriya Janar Yakubu Gowon

Tuna Baya: Tarihin shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Aguiyi Ironsi

Shi ya ƙirƙira ƙarin jihohi shida inda ya mayar da su daga 12 zuwa 19.

Shi ne kuma ya zaɓi Abuja ta zama sabon Birnin Tarayyar Najeriya domin kaucewa matsalolin da ake fama da su a Legas.

Ga shi kuma ya yi aiki babu sani babu sabo, ba kasala ba jan ƙafa wurin yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya binciki ministoci da gwamnoni na gwamnatin da ya gada kuma ya ƙwato kadarorin da suka sata.

Ya kuma sallami dubunnan ma’aikata da ya samu da laifi ko ya fahimci ba a buƙatarsu.

Tuna Baya: Tarihin Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa

Sai dai ana ganin wannan matakin shi ne ya tashi hankalin waɗanda suka rage suka shiga tafka rashawa don shirin ko-ta-kwana.

A ɓangaren ƙasashen ƙetare ya lakace hahncin Turawan Yamma inda ya soki yadda suke katsalandan cikin harkokin Afirka.

Har yanzu akwai waɗanda suke ganin da haɗin bakin Amurka aka shirya masa juyin mulki saboda ya kawo mata cikas wurin cimma manufofinta.

Bayan da aka kashe shi a juyin mulkin da bai yi nasara ba, ƴan Najeriya sun shiga jimami da matsanancin alhini.

Kuma domin tunawa da shi a ka sanyawa babbar tashar jiragen sama dake Legas sunansa kuma aka ƙirƙiro Naira Ashirin domin karrama shi.