✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tuna Baya: Tarihin shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Aguiyi Ironsi

Manjo Janar (Sir) Johnson Thomas Umunakwe Aguiyi Ironsi shi ne shugaban mulkin soji na farko a tarihin Najeriya kuma shugaban ƙasa na  biyu bayan samun…

Manjo Janar (Sir) Johnson Thomas Umunakwe Aguiyi Ironsi shi ne shugaban mulkin soji na farko a tarihin Najeriya kuma shugaban ƙasa na  biyu bayan samun ƴancin kai.

Janar Ironsi ya  mulki ƙasar nan tsawon watanni shida ne kawai daga watan Janairu zuwa watan Yulin 1966.

Wannnan jarumin soja da ya yi fice a fagen fama, kuma ya yi fama da ƙalubale wurin tafiyar da mulkin al’umma.

Tuna Baya: Tarihin Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa

Ya karɓe ragamar mulki ne bayan da ya  murƙushe  juyin mulkin da wasu hafsoshin soji ƴan tawaye suka shirya wa gwamnatin farar hula.

Sai dai matakan da ya ɗauka a zamanin mulkinsa sun jawo masa bore daga sojin Najeriya inda suka hallaka shi yayin juyin mulkin ɗaukar fansa.