Dokta Goodluck Ebele Jonathan shi ne shugaban farar hula na farko a tarihin Najeriya da ya fadi zabe yana kan kujerar mulki.
Ya zama gwamnan Jihar Bayelsa bayan an tsige Gwamna Alamiyaseighya, sannan ya zama shugaban kasa a sanadiyyar rasuwar Shugaba Ƴar’adua a kan mulki.
Ya mulki Najeriya tsawon shekaru biyar inda ya sha fama da adawa da tsangwama. Kuma a zamaninsa kungiyar Boko Haram ta yi karfi har ta kwace mulki da wasu sassa na Najeriya.
Ya yi nasara a zaben 2011 amma ya fadi a zaben 2015.
Sai dai kuma ya kafa tarihi a wannan faduwar kasancewar tun kafin a sanar da sakamako, ya sallama, ya taya wanda ya ci zabe murna.