✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tun shekarar 2003 na san Cristiano Ronaldo zai zama fitaccen dan kwallo – Giggs

Tsohon dan wasa kwallon kafa ta Manchester United kuma mataimakin mai horar da ’yan wasan kungiyar Ryan Giggs ya ce lokacin da ya ga Cristiano…

Tsohon dan wasa kwallon kafa ta Manchester United kuma mataimakin mai horar da ’yan wasan kungiyar Ryan Giggs ya ce lokacin da ya ga Cristiano Ronaldo na buga wasa a wasan sada zumunta tsakanin kungiyar Sporting da Manchester United a shekarar 2003 ya san cewa wata rana Ronaldo zai zama babban dan wasa.
Giggs wanda ya shafe shekara shida a kungiyar Manchester United tare da Ronaldo kafin ya koma kungiyar Real Madrid ya ce “Lokacin yana matashi, amma sai na ga yadda yake juya John Oshea wanda hakan ya sa na yi wa John Oshea dariya ganin yadda yake shan wahala wurin karamin yaro.
Bayan wannan wasan ne kungiyar ta Manchester United ta yi zawarcin Ronaldo domin ya ci gaba da buga wa kungiyar. Kuma daga nan Cristiano Ronaldo ya amince ya dawo kungiyar inda ya buga wa kungiyar kafin ya koma Real Madrid da ke kasar Spain inda yake bugawa a yanzu.
A ranar Lahadi da ta gabata ce Cristiano Ronaldo ya zubar da hawaye bayan da kasarsa ta Portugal ta kafa tarihin lashe Kofin Nahiyar Turai a karo na farko, bayan ta doke Faransa da ci daya mai ban haushi a wasan karshe.
Ronaldo ya fita daga wasan bayan da dan wasan Faransa, Dimitri Payet ya yi masa ketar da ta jawo yi masa rauni, sai dai da Ronaldo ya koma bayan fili sai ya rika shiryar da ’yan wasan, inda a wasan karin lokaci dan wasan gaba na kungiyar Lille, Eder ya auna wata kwallo daga yadi na 25 ta shige ragar Faransa a wasan da suka buga a filin wasa na Stade de France.
Portugal ta samu wannan nasara ce bayan shekara 12 da ta sha kashi a hannun kasar Girka da ci daya mai ban haushi lokacin da ta karbi bakuncin gasar a shekarar 2004, sai ga shi ta rama wannan lamari a kan Faransa.
kasar Portugal ta samu nasara a kan Faransa har sau 10 a jere, bayan da Faransar ta yi waje da Portugal a wasan kusa da na karshe a gasar Nahiyar Turai da aka buga a 1984 da ta shekarar 2000 da kuma gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2006.