Mutane da dama sun san shi da lakabin Angon Sambisa saboda ya fito a bidiyon wakar nan ta ‘Sambisa’ wadda ta shahara a kafofin sada zumunta na zamani.
Ko da yake ba ‘Sambisa’ ce kadai wakar da Ibrahim Yamu Baba ya hau ba, ita ce wadda ta sa ya fi shahara.
A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana rawar da yake takawa a harkar fim da waka.
Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarka?
Ibrahim Yamu Baba: Ni dai asalinmu mutanen Biu ne da ke Jihar Borno.
- Yadda muka shirya bidiyon wakar Sambisa —Darakta Abubakar 3SP
- Yadda wakar Hausa ta Sambisa ta tayar da kura
Mahaifina dan boko ne, ya zo ya zauna a nan garin Jos, kuma aka haife ni a wannan gari, na girma har na yi karatu, har na fara wannan sana’a ta fim da waka.
A ina ne ka samo wannan suna na Yamu Baba?
Wannan suna ya samo asali ne daga unguwar da nake zaune a nan Jos, wato Gangare.
A nan ne wani mutum, ana kiransa Lawal, saboda ya gan ni fari, sai yake kira na Inyamuri.
To daga nan da na fara girma, sai aka yi wa wannan suna kwaskwarima, aka ci gaba da kira na Yamu Baba.
Ya zuwa yanzu ka kai kamar shekara nawa da fara wannan sana’a?
Na kai shekara 15 ina yin wannan sana’a.
Ka shahara a wakar Sambisa — shin akwai wasu wakoki da ka taba fitowa, ko a wakar Sambisa ka fara fitowa?
Akwai wakoki da yawa da na fito, akwai wakokin Suwaiti da Alkawarin Kauna da dai sauransu.
Marubucin wakokin Sambisa ya yi barazanar cewa ba zai ba ku wakoki na gaba ku yi bidiyonsu ba. Yaya za ka ji idan aka ce yau ga wata wakar Sambisa, amma ba kai ne a bidiyon ba?
Gaskiya wannan tambayar ta ba ni dariya, domin ni ban taba jin wannan labari ba.
Kuma idan marubucin wannan waka ya ce zai hau wakarsa wannan ba matsala ba ce domin duk wanda yake wannan sana’a, burinsa ne ya ga ya samu daukaka kuma an san shi.
Don haka ba matsala ba ce idan ya ce zai hau wakarsa, domin dama ana yin irin wannan, ka ga ainihin mawaki ya hau wakarsa.
To ni jarumi ne duk abin da aka ba ni, ina kokarin na ga na hau na zauna a kai. Don haka ni a wurina, wannan ba matsala ba ce.
A baya-bayan nan an gan ka a bidiyon sabon salon wakar ‘Jarumai’ ta Yakubu Muhammad. Mene ne labarin wannan waka?
Labarin wannan waka ya samo asali ne — akwai wasu mawaka ne su biyu, daya yana Kaduna sunansa Nakabala, dayan kuma Adamu.
Su ne suka shirya wannan waka, suka gayyace mu ganin mu ne za mu iya hawa kan wannan waka, mu ba su abin da suke so.
A wadanne fina-finai ne ka fito?
Fina-finan da na fito sun hada da ‘Rabin Raina’ da ‘Bakin Mulki’ da ‘Ana Musulim’ da dai sauransu.
Akwai kuma wasu sababbin fina-finai da na fito a cikinsu, wadanda suka hada da ‘Gaushi’ da ‘Sarkakiya’ wadanda ba a sake su ba.
Da bidiyon waka da fim wanne ka fi so ka yi?
Wallahi dukkansu ina yi, kuma dukkansu ina son su.
Ni dai burina a kullum na ga na yi wa masoyana abu mai kyau.
Mene ne matsayinka kan harkar waka?
Gaskiya ni mawaki ne sosai domin ina wakokin aure da siyasa.
Ko a kan me ka sa ni na yi maka waka zan iya yi. Sai dai ba na wakokin fim, amma duk wani abu da ka bukaci na yi maka waka a kansa zan yi.
Wakar siyasa ko wakar barkwanci duk ina yi. Kuma ina hawa wakokin wasu mawaka saboda ni jarumi ne, don haka duk wakar da aka ce na hau zan iya hawa.
Domin idan kai jarumi ne, duk abin da aka sanya ka ka yi, za ka yi kokari ka ga ka yi wannan abin.
Duk wanda ya san ni ya san ni mawaki ne.
Wanne ka fi jin dadi tsakanin waka da fim?
Gaskiya dukka ina jin dadinsu, amma a yanzu dai waka ce take kawo mani kudi. Babu shakka fim yana kawo mani kudi, amma waka ta fi kawo mani kudi fiye da fim.
Wane ne gwaninka a harkar fim ko waka?
Gaskiya tsakani da Allah, a harkar waka ba ni da wani gwani. Domin abin da ya ba ni damar yin waka, muna da studio da kayan aiki da makadin wakoki.
Ganin mun saba ko da yaushe, a hankali har mu ma muka goge. Don haka gaskiya ni ba ni da wani gwani kan harkar waka.
Amma a harkar fim tsakani da Allah gwanina shi ne Ali Nuhu.
Daga lokacin da ka fara wannan sana’a zuwa yanzu, wadanne irin nasarori ne ka samu?
Gaskiya na samu nasarori da dama a wannan sana’a, domin na samu lambobin karramawa da dama, daga kamfanoni, misali a baya-bayan nan na samu lambar yabo daga kamfanin Itel.
Bayan haka ta dalilin wannan sana’a, na mallaki wasu abubuwa da dama na rufin asiri.
Mene ne burinka a wannan sana’a?
Babban burina a wannan sana’a shi ne na samu daukaka, na samu arzikin da ke cikinta, na samu wata gidauniya da zan rika taimaka wa al’umma gajiyayyu da marasa karfi.