✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tun 2016 aka gano COVID-19 za ta bulla, amma aka yi sakaci

Bayan shekara hudu an ki daukar rahoton binciken da aka gudanar da muhimmanci.

Wani bincike ya gano cewa tun shekarar 2016 masana kiwon lafiya suka yi gargadi game da yiyuwar barkewar annobar COVID-19 amma hukumomi suka ki daukar matakan da suka dace.

Tun a wancan lokacin masana kiwon lafiya da suka gudanar da binciken a kasar Birtaniya suka ba da shawarar a tanadi kayayyakin kariya (PPE) da kuma sanya ido da bincika lafiya daga nesa ga masu shige da fice a kasar.

Wannan na kunshe ne cikin rahoto mai shafi 23 da aka fitar, Exercise Alice, wanda tun daga lokacin ake ganin sakacin hukumomin Birtaniyar ya sa annobar coronavirus ta’azzara a yankin kamar yadda jaridar The Guardian ta wallafa.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Birtaniya a wancan lokaci, Dame Sally Davies, wanda babban likita ne ya kaddamar da aikin binciken, wanda shi da jami’ai Hukumar Lafiya ta (NHS), da masu sa ido a harkar lafiya suka gudanar.

  1. – Abin da binciken ya gano

Rahoton binciken ya yi hasashen cewa za a samu barkewar wata cuta  mai kama da zazzafar murar MERS a birnin Landan da kuma Birmingham na kasar.

Yanayin cutar MERS na kama da cutar COVID-19, ta yadda take sarke numfashi tare da yaduwa cikin gaggawa kuma ba ta da wani sanannen maganin ko rigakafi.

Wannan ya sa hukumomin gwamnati a lokacin suka karkata kan ganco cutar, ba tare da mai da hankali yadda ya kamata ba wajen daukar matakan da samar da kayan kariya (PPE).

Jami’an lafiyar da suka gudanar da binciken coronavirus na 2016 sun yi amannar cewa samar da wadatattun PPE “na da matukar muhimmanci ga ma’aikatan lafiya.”

  1. – Shawarar masu bincike

Rahotonsu ya ba da shawara cewa “A tanadi adadi adadi mai yawan gaske na PPE saboda ko da an samu bullar cutar ba za a samu karancinsu ba.”.

Ya kuma bayyana karara cewa dole a inganta “tantance lafiyar mutane a tashoshin shigowa ko fita daga kasar” domin dakile yaduwar cutar daga kasashen ketare

“Sannan jami’an lafiya su ba da shawarar “ba da tazara ko killace kai idan aka samu alamar cutar, har ga mutanen da alamarta ba ta bayyana a jikinsu da wadanda ke fuskantar barazanar kamuwa da ita.”

Binciken ya kuma jaddada cewa kasar na bukatar samar da ingantattun hanyoyin gano cutar da kuma mutanen da suka yi mu’amala da masu ita.

Sun kuma ba da shawarar yin “amfani da manhajar intanet … ko rumbun tara bayanan mutanen da suka yi mu’amala kai tsaye da dai sauransu”.

  1. – Sakacin gwamnati

Bayan fitowar rahoton a watan Agusta, gwamnatin Birtaniya ta ki sakin sa ga jama’a, saboda gudun karya wa jama’a gwiwa game da shirinta da na NHS game da annobar.

Yawancin abubuwan da rahoton na Alice Exercise ya yi hasashe sun wayi gari a matsayin manyan matsloli a farko-farkon bullar cutar COVID-19 a Birtaniya.

Misali, a watan Maris na 2020, ma’aikatan lafiya sun koka game da tsananin karancin kayan kariya (PPE), lamarin da ya haifar da damuwa cewa suna yada cutar fiye da kima.

Hakan ne kuma ya sa aka yi ta rige-rigen samar da kayan kariyar da suka dace, ganin yadda mace-mace masu cutar ke ta karuwa a lokacin.

Baya ga haka, hukumomin Birtaniya sun yi ta barin baki suna shigowa kasar, hatta daga kasashen da COVID-19 ta yi kamari irin su China da Italiya, sabanin shawarwarin binciken Exercise Alice.

Ana ganin cewa da hukumomin sun yi amfani da matakan, da lamarin bai yi kazancewar da mutum 1,000 ke mutuwa a kullum ba a lokacin kullen farko a watan Mayun 2020 a Birtaniya.

  1. – Rahoton ya shiga intanet

Duk da cewa gwamnatin Birtaniya ta nemi ta boye rahoton, dole  aka ba wa wani Dokta Moosa Qureshi rahoton, bayan ya matsa lamba karkashin dokar ’yancin samun bayanai, daga bisani kuma shi Qureshin ya dora rohoton a intanet.

Ana ganin fitar rahoton zai sa gwamnati ta kara bincike a kan annobar da kuma kuma yadda za a shawo kanta.