Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel, ya tsawaita kwataraginsa da kungiyar wanda zai ci gaba har zuwa shekarar 2024.
Sabuwar yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu na zuwa bayan da Tuchel ya samu nasarar daukar wa Chelsea Kofin Zakarun Turai a bana.
- Kotu ta ba da umarnin rage albashin ’yan Majalisar Tarayya
- ‘Babu shirin bai wa masu yi wa kasa hidima horon tafiya yaki’
A bara ce Tuchel ya karbi ragamar horar da Chelsea yayin da take matsayi na 9 a teburin gasar firimiyar Ingila, inda a halin yanzu ya taimaka mata wajen kare gasar a matsayi na hudu gami da lashe gasar Zakarun Turan bayan ya doke Manchester City a wasan karshe.
Kazalika, Tuchel ya maye gurbin Frank Lampard bayan kungiyar ta raba da gari da shi sakamakon rashin yi mata wani katabus.
A yanzu Tuchel bayan kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar ya bayyana farin cikinsa tare da maraba da matakin da ta dauka na bashi damar ci gaba da horar da ’yan wasanta.
Ita ma kungiyar ta sanar da farin cikinta na tsawaita kwantaraginsa na karin shekaru biyu doriya a kan na watanni 18 da ta bashi karon farko bayan rawar da ya taka cikin watanni shidan da suka gabata.
A watan Dasimbar bar ace kungiyar PSG ta sallami Tuchel bayan ya kai ta wasan karshe na gasar Kofin Zakarun Turai ya kuma lashe mata gasar Ligue 1 har sau biyu.