A yau muna dauke ne da tsokacin Shugaban Hukumar Editocin Jaridun Daily Trust, Malam Mahmud Jega kan tube Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Editanmu Salihu Makera (07086866165) ya fassara kamar haka:
Kusan kowane mai lura da al’amura ya san haka za ta faru, doguwar dambarwa a tsakanin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, lokacin kadan za ta sa a tube Sarkin daga gadon sarautar mai dogon tarihi. Kuma kusan kowa bai ji mamakin abin da ya faru a jiya (Litinin) ba.
Tun bara Ganduje da gwamnatinsa ta APC suka tasa Sanusi a gaba. Mukarraban Gwamnan da sauran ’ya’yan jam’iyyar sun ci zarafin Sarkin a bainar jama’a. An rurrubta takardun koke-koke wasu daga sanannun mutane ko kungiyoyi wasu na giri ana neman hukumomi su binciki zarge-zargen aikata ba daidai ba daga Sarkin da Majalisar Sarki. Hukumar Karbar Koke-Koken Jama’a da Yaki da Almundahana ta Jihar a karkashin wani mai azarbabi, Muhuyi Magaji Rimin Gado ta amshi batutuwan inda ta yi ta sammacin manyan jami’an masarautar daya bayan daya. Majalisar Dokokin Jihar da APC ta mamaye ma ta karbi korafe-korafe ciki har da wanda a makon jiya ya zargi majalisar masarautar da sayar da wasu gandun Sarki.
Babban naushi da Sarki Sanusi ya sha, shi ne na watan Disamban bara, lokacin da Gwamnatin Jihar ta kirkiro sababbin masarautu hudu a Bichi da Rano da Karaye da Gaya. Masarautar Sanusi da take da kananan hukumomi 44 an rage ta zuwa 10. A wani lokaci ma gwamnatin ta yi yunkurin mayar da shi Sarkin Birnin Kano, wanda hakan ke dusashe hasken Masarautar Kano mai shekara 500.
Me ya jawo wadannan abubuwa? Zahiri abu biyu ne. Na daya halayen Sanusi na zamananci da ya haifar da bambancin da ke kamar tsakanin sama da kasa da wanda ya gada a shekarar 2014 wato Alhaji Ado Bayero. Yayin da Ado Bayero ya kame bakinsa kuma ya ja amawali ya rufe a tsawon shekara 51 a gadon sarauta, Sanusi kuma ya cika halartar tarurruka yana zuba a tarurrukan. A al’adar Arewa, galibi Sarki kan karfafa jama’a ne ya yi addu’ar zaman lafiya, amma Sanusi sai ya zamo bako mai jawabi a irin wadannan tarurruka. Kuma sabanin matsayinsa yakan dauki dogon lokaci yana jawabi, ya rika muhawara da masana yana kawo misalai da kididdigar Bankin Duniya da hukumomin tattalin arziki na Turawan Yamma da ’yan falsafa Musulmi da sauransu. Tsarinsa ya sha bamban sosai da na dukkan sarakunan Arewa wadanda galibi sukan kame bakunansu daga magana a taron jama’a.
Kuma Sanusi yakan fito bainar jama’a ya rika magana irin wadda malaman jami’a da ’yan kungiyoyin gwagwarmaya da marubuta a jaridu ne kawai suke yi. Ya taba bayyana cewa Arewacin Najeriya na riko ne da tsarin Musulunci na Karni na 13, lamarin da ya harzuka malamai da masu ra’ayin mazan jiya. Ya rika sukar al’adar auren mata da yawa ga talakawa da kuma haihuwar ’ya’ya masu yawa. Ya ce, wannan al’ada ce take talauta galibin ’yan Arewa. Irin wannan magana galibi malaman jami’a ne suke fadi, kuma fitowarta daga bakin Sarki daga Arewa ta jawo rashin jin dadi a tsakanin masu ra’ayin mazan jiya. Kuma a farkon bana Sanusi ya fada wa iyayen da aka sace ’ya’yansu cewa su ya kamata a kama, saboda sun yi sakaci sun bar ’ya’yan suna fita waje ba tare da sanya ido a kansu sosai ba. Kuma ya taba fitowa a gaban jama’a ya ce, Ganduje da ’yan Majalisar Dokokin Jihar sun kwashe wata daya a China suna neman a yi titin jirgi. Su kuma suka ce kwana hudu kawai suka yi.
Sakin bakin Sanusi ya rika jawo masa farin jini a Kudu da kafafen watsa labaransu. Kuma a tsarin siyasar Najeriya duk abin da yake burge mutanen Kudu zai yi wuya ya samu karbuwa a Arewa haka abin da ke burge mutane Arewa bai karbuwa a Kudu. Matasan Arewa da dama sun fadi a shafukan sadarwa zamani cewa tsohon dalibin na Kwalejin Kings College da ke Legas yana kokarin burge mutanen Kudu ne koda hakan zai cutar da jama’arsa na Arewa. Wannan kuma ba abu ne da zai taimaka masa ba.
Sannan yana iya zama a gadon sarautarsa ba domin ya tsoma kansa a cikin siyasar jiharsa ba. Gwamna Ganduje da jiga-jigan APC a Kano suna da yakinin cewa Sanusi dan PDP ne kuma ya yi matukar goya mata baya, wadansu ma sun ce ya ba dan takarar Gwamnan PDP Abba Kabir Yusuf (Gida-Gida) kudi. A fili dai babu wanda ya san wace shaida Ganduje da magoya bayansa suke da ita game da fada da Sarkin ba, amma akwai yiwuwar sun samu cikakkun shaidu daga ’yan siyasa kila ma da wadansu fadawan Sanusi. Kuma alamar akwai rigima ta fara bayyana ce a ranar da aka bayyana Ganduje ya samu nasara bayan zaben da ke cike da takaddama na sake zaben mazabar Gama a bara, inda daruruwan magoya bayansa suka shiga dakin taro na Gidan Gwamnati suka hau kwaranga suka jefo hoton Sarkin daga jikin bango suka tattake shi.
Lokacin da rikicin baya-bayan nan ya kaure tsakanin Ganduje da Sanusi a bara, gwamnonin Arewa da fitattun manyan sarakunan Arewa a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar sun koma gefe. A cewar wani Gwamna hakan ya faru ne saboda a shekarar 2017 sun sulhunta mutanen biyu, amma ga shi sun koma fagen daga. Kuma sun zargi Sanusi da rushe sulhun, inda suka ce ya keta mafi yawan ka’idoji da shawarwarin da aka cimma a taron sulhu a Kaduna.
Mashwaratan Ganduje ma sun taka rawa sosai a rigimar. Sun riga sun yanke shawarar kawai a tube Sarkin tun suna mulki, domin zai iya yi musu illa idan suka bar mulki. Wannan ya sa a daren da gwamnoni da sarakuna Arewa suka yi sulhun farko a shekarar 2017, Ganduje ya hadu da adawa daga wadansu manyan mukarrabansa, wadanda suka zarge shi da mika wuya ga matsin lamba. Wadansu daga cikinsu sun ce tunda suna fuskantar adawa mai hadari daga Kwankwasiyya da jagoranta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, to su rage makiyansu ta hanyar tube Sanusi.
Sannan magoya PDP a Kano ma sun tabarbara lamarin Sanusi, ta hanyar zuwa neman goyon bayansa. Duk lokacin da ya fito bainar jama’a matasan da Ganduje ke da yakinin magoya bayan Kwankwasiyya ne kan yi tururuwa jikin motarsa suna yi masa maraba ta musamman. Jiya (Litinin) kafin Majalisar Zartarwa ta tube Sanusi an gabatar da kudiri a Majalisar Dokokin Jihar ana kiran a dakatar da Sarkin, inda wakilan PDP a majalisar da suke sanye da jar hula suka dauke sandar majalisa. Wannan ya sa da niyya ko rashin niyya, Sanusi ya fada tsundum a cikin mummunan rikicin siyasar Kano tsakanin APC da PDP, inda karshen ya zamo mai muni.
Har wa yau Sanusi II ya fara samun babbar matsalar siyasa ce mafi girma da Shugaba Muhammadu Buhari. Tun a shekarar 2015, Sanusi yake sukar tsarin tattalin arziki na gwamnatin Buhari a wuraren taro, wani lokaci ma ya ce gwamnati ba ta da tsarin tattalin arzikin. Ya taba cewa da gwamnatin ta dauki matakan da suka dace da kasar nan ba ta shiga masassarar tattalin arziki a 2015 ba saboda faduwar farashin man fetur. Wata biyu da suka gabata Ganduje ya jagoranci manyan ’ya’yan Jihar Kano suka kai ziyara gaBuhari a Abuja, amma Sunusi bai cikin ayarin. Kuma Buhari ya fadi a lokacin cewa ba zai tsoma baki a rikicin Kano ba, saboda a karkashin tsarin mulkin 1999, Shugaban Kasa ba ya da wata rawar takawa kan al’amuran masarautu. Jawabin ya kashe gwiwar wadansu shugabannin Arewa a karkashin tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalami Abubakar da suke kokarin sulhuntawar da ake cewa da sunan Buhari suke yi. Ga masu lura da al’amura da dama jawabin na Buhari nuni ne ga Ganduje ya tube Sarkin.
Lamarin mai kama da juyin mulkin a jiya (Litinin) na sanar da tubewar, a fili manufarsa a hana kotuna tsoma baki da sunan dakatar da batun. Domin tun bara magoya bayan Sanusi suka rika samun dakatar da binciken da ake yi kan Sanusi ko kowane yunkuri a kansa. Wasu daga cikin dakatarwar daga baya an dage su, kuma a abin da ya shafi kirkiro sababbin masarautu Majalisar Jihar ta sake dubawa ta yi gyara kan hanyar da ta bi.
Ba abin mamaki ba ne da Ganduje ya hanzarta nada sabon Sarkin Kano kafin kotu ta tsoma baki. Aminu Ado Bayero Sarkin Bichi dan marigayi Sarki Ado Bayero ne aka nada sabon Sarkin. Masu lura da al’amura sun sa ran yiwuwar wannan zabi, domin amincewar da Aminu Ado Bayero ya yi ta zama Sarkin Bichi duk da rashin amincewar ’yan uwansa wadanda suka ce kada ya taimaka a tarwatsa Masarautar Kano, hakan ya dadada wa Ganduje wajen tabbatar da halaccin sababbin masarautun, don haka yanzu lokaci ya yi da za a saka masa. Duk da yanayin yadda ya haye karaga, Aminu Ado Bayero na iya zama zabin da jama’a suka fi so, saboda tsohon dalibin na Jami’ar Bayero mutum ne na mutane kuma ya kasance na kusa da mahaifinsa marigayi Sarki.
A yammacin Litinin ne Gwamnatin Jihar Kano ta sa ’yan sanda suka fito da tsohon Sarki Sanusi daga fada suka dauke shi zuwa Jihar Nasarawa don a zaunar da shi a wani lungu a takaita zirga-zirgarsa. Wannan shi ne abin da ake yi tun zamani mulkin mallaka, inda Turawan Birtaniya suka kai sarakuna da dama da suka tube zuwa Lakwaja, sai dai akwai yiwuwar Sanusi ya kalubalanci kai shi wani gari, wanda haka ya ci karo da tsarin mulkin 1999.
Muhammadu Sanusi ya zamo babban Sarkin Arewa na uku da aka tube tun daga 1996. Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki aka fara cirewa a 1996, sai Sarkin Gwandu Almustafa Haruna Jokolo da aka tube a shekarar 2005. Wadannan su ne sarakunan Arewa mafiya girma a jeri (in baya ga na biyu Shehun Borno) wadanda aka tube a cikin shekara 25.
Tube Sanusi wani abin bakin ciki na biyu ne ga danginsa, idan aka dubi tarihi kakansa Sarki Muhammadu Sanusi I, Gwamnatin Jihar Arewa ta tube shi a 1963 bisa dogaro da kwamitin bincike na Muffet kan harkokin kudin Masarautar Kano. Muhammadu Sanusi II ya hau gadon mulki ne shekara 51 bayan haka, lamarin da wadansu Kanawa ke ganin wanke kakansa ne. Yanzu da aka tube shi masu ra’ayin mazan jiya za su iya daukar haka a matsayin wata gazawa ce a cikin iyalan Sanusi.
Wadansu masu lura da al’amura suna cewa tubewar tana iya zama gobarar Titi, saboda Sanusi na iya shiga siyasa ya yi kwarjinin da ba a zato a takarar Shugaban Kasa a shekarar 2023, wannan lokaci ne zai nuna. Sannan ga Gwamna Ganduje da mukarrabansa yanzu za su fara tunanin yadda za su magance matsalar da suka haifar ta kirkiro masarautu hudu a bara. Sabon Sarki Aminu Ado Bayero ba zai so su ba, duk da cewa yana daya daga cikin sababbin sarakunan. Yanzu dai an zuba ido a ga hanyar da za su warware wannan matsala.