A yayin da muka kammala watan azumin Ramadan, muna gabatar da wannan fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki ta Sallah kamar haka:
Zakkar Fidir:
Zakatul-Fitr ko Zakkar Fid-da-Kai, ita ce sadakar da ake fitarwa a karshen azumin watan Ramadan. Sunnah ce wajiba a kan kowane Musulmi namiji da Musulma mace, babba da yaro, da da bawa, ana so ya fitar da ita ko a fitar masa kafin zuwa Sallar Idi.
Kuma ya halatta a fitar da ita kwana uku ko biyu ko daya kafin ranar Sallar Idi Karama don a ba fakirai da miskinadamar sarrafawa su yi farin ciki a ranar Idin.
Mai gida zai fitar wa kansa da kananan ’ya’yansa da dukkan wadanda suke
karkashinsa sai dai in suna da dukiyar da za su iya fitar wa kawunansu.
Manzon Allah (SAW) ya wajabta ta a kan Musulmi kowa ya fitar da Sa’i daya (Mudun Nabiyyi hudu) na dabino ko alkama ko irin abincin da muke da su kamar shinkafa da masara da dawa da gero.
Kuma ana raba ta ce ga miskinai (wadanda ba su mallaki abincin wuni ba) da fakirai (wadanda ba su mallaki abincin shekara ba) da sauran raunana da mabukata.
Kuma duk wanda ya fitar kafin zuwa Idi shi ne ya yi Zakkar, wanda kuma bai fitar ba sai bayan Idi, ya yi sadaka ce kamar sauran sadakoki, hakan ya tabbata a Hadisi.
Sallar Idi da ladubbanta:
Malamai sun hadu cewa ta kowane hali a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara kamar yadda Imam Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15).
Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumin kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya wa bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).
Sannan Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wadanda suka fi kyau a sa, kuma a fesa turare a fita Masallacin Idi, maza da mata manya da yara tare da tsare ladubban fitar, wato kada mata sun caba ado ko su sanya turare kuma kada a cakuda maza da mata da sauran abubuwan da shari’a ta hana.
Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin
ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen
murna a wuce gona-da-iri. Kada murna
ta sa a yi sabo. Kada murna ta sa a aikata bidi’o’in da za su vata kyawawan ayyuka.
Wannan shi ne makasudin bijiro da wasu daga cikin ladubban da suka kamata mu yi don murnar wannan rana da masu biyo ta, kamar haka:
1. Taya juna murna da duk lafazin da ya sauwaka, kamar “Allah Ya karba mana da makamancin haka.
An ruwaito cewa wadansu daga magabatan kwarai suna aikata hakan. Misali Jubairu bin Nufair ya ce, “Sahabban Annabi (SAW) idan suka hadu da juna sukan ce, “Allah Ya karba mana, Ya karba muku.”
Imam Ahmad ya ce Isnadinsa mai kyau ne, sannan Hafiz Ibn Hajar ya kyautata Isnadinsa a cikin Fathul Bari (2/517), a duba Tamamul Minnah na Albani don karin bayani.
Kuma an ruwaito Imam Ahmad yana cewa: “Ba zan fara fada wa mutum haka ba, amma idan ya fada min zan amsa masa.”
Shi kuma Shaihul Islam Ibn Taimiyya (Rahimahullah) ya ce, “Fara taya murna ba Sunnah ce da aka yi umarni da ita ba, kuma ba a hana ba, wanda ya aikata, ya yi koyi wanda ya ki, ya yi koyi.” Majmu’u Al Fatawa (24/253). Hakika irin wannan gaisuwa tana yin tasiri wajen karfafa zumunta da ruhin soyayya a tsakanin Musulmi.
2. Ziyartar ’yan uwa da makusanta domin sada zumunta. Wannan mustahabbi ne a kowane lokaci, amma an fi karfafa shi a irin wannan lokaci, musamman ziyartar iyaye, domin ana sanya musu farin ciki, kuma haka cika umarnin Allah ne na a kyautata musu.
3. Wadata abinci da abin sha: Babu laifi a wadata abinci da abin sha a wadannan ranaku ga iyalai ba tare da almubzzaranci ba, saboda Hadisin Anas a wurin Abu Dauda da Nisa’i bisa Isnadi ingantacce da ya ce: “Lokacin da Annabi (SAW) ya isa Madina, ya iske suna taruwa ranar idoji, sai ya ce, “Kuna da yini biyu da kuke wasanni a cikinsu, to, haqiqa Allah Ya musanya muku da mafiya alheri: Ranar Karamar Sallah da Ranar Layya.”
Kuma kuyangi ko yara mata suna iya
yin wake-waken da suka halatta, saboda Hadisin A’isha (RA) cewa, “Manzon Allah (SAW) ya shiga wurina ina tare da wadansu kuyangi biyu suna kida da waka (wadansu sun ce da shantu) sai ya kishingida a kan tabarma ya juya fuskarsa.
Sai Abubakar (RA) ya shigo ya yi min fada ya ce “Shaidan a gidan Annabi (SAW)? Sai Manzon Allah (SAW) ya kalle shi ya ce “Kyale su-a wata ruwayar ya ce “Ya Abubakar ko wadanne mutane suna da Idi, wannan Idinmu ne.”
Wasu bidi’o’i da ake yi lokacin bukukuwan Idi
1. Wadansu kan kirkiro ayyuka na raya Daren Idi da ibada bisa dogaro da hadisan da ko dai masu rauni ne ko na karya.
2. Ziyartar makabarta, wannan ya saba wa manufar Idi na nuna farin ciki da jin dadi, domin a cikin zuwa makabarta akwai nanata bakin ciki, kuma hakan ya saba wa shiriyar Manzon Allah (SAW) da ayyukan magabatan kwarai.
3. Sai cudanya tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwan. Wannan babbar fitina ce, mai hadari da ta wajaba shugabanni da malamai su hana, kuma ya kamata Musulmi manya da matasa su riqa jira mata su bar masallatai kafin su tashi bayan idar da Sallah.
4. Fitar mata sanye da turare cikin ado: Abin da ya zamo wajibi shi ne mahaifa da waliyan mata su rika umartarsu da suturce jiki da sa hijabi da lizimtar ladubban fita daga gida tare da gargadinsu kan auka wa abin da zai fusata Allah. Idan ba za su tsare hukunce-hukuncen shari’a ba, to wajibi ne su hana su fita masallacin gaba daya.
5. Sauraren kaxd-kade da wake-waken da suke haramta. Kila wadansu na iya fakewa da Hadisin kuyangi biyu su rika
aikata abin da yake haram.
Manzon Allah (SAW) ya ce, “Za a samu wadansu mutane a cikin al’ummata da za su rika halatta zina da alhariri da giya da wake-wake da kayayyakin kade-kade.” Wake-wake da kayayyakin kade-kaden da suka saba wa shari’a wajibi ne a guje musu.
6. Wasa da Sallah. Babban abin bakin ciki shi ne mutane da yawa suna wasa da Sallah a cikin jama’a ko su yi barci ba su yi Sallar ba, saboda sun bata lokacinsu wajen hira ko wasanni sun gaji a ranakun Sallah.
Allah Ka tabbatar da mu a kan imani
da aiki nagari, Ka rayar da mu rayuwa mai tsabta, Ka riskar da mu ga salihai, Ka sanya iliminmu ya zamo don neman yadarKa da kusantarKa, mai amfanarwa ga bayinKa, Ka jibince mu a duniya da Lahira, Ka shiryar da mu zuwa ga gaskiya da izininKa, lallai Kai Kana shiryar da wanda Ka so zuwa ga tafarki madaidaici.