Wani tsuntsu mai suna Black egrets, wanda jinsin wasu tsuntsaye ne da ake samu a Nahiyar Afirka, yana da wata dabara ta musamman wajen farautar abincinsa ta amfani da fika-fikansa su koma kamar lema.
Fika-fikan ba kawai suna janyo kifiye don samun lemar ba ne ba, har ma suna sa su samu tsaro.
- Hisbah ta nemi Saudiyya ta tallafa mata wajen horar da jami’anta
- Hatsari: Ganduje ya yi alhini kan mutum 17 da suka rasu a Kano
Tsuntsun kan yi lema kamar bado a saman ruwa kuma ana kiran hakan da ‘canopy feeding’ wadda dabara ce ta farautar da bakaken tsuntsayen ke amfani da ita ta zama daya daga cikin abubuwan da ake iya ganowa a daji.
Bakaken tsuntsaye suna yawo a hankali a saman ruwa mara zurfi sannan suna shimfida fika-fikansu, don samar da lema iri-iri wacce ke toshe hasken rana.
Kodayake ba a bayyana dalilin da ya sa wannan jinsin tsuntsaye da ke Nahiyar Afirka ke amfani da wannan dabara ba, sai dai masana kimiyya sun ce, yin hakan na da fa’idoji da yawa, kamar rage haske da jawo kifin cikin tarko.
Wani abu da aka yarda da shi, shi ne cewa, kananan kifayen da ke neman wurin buya daga masu yi masu illa na shiga wannan tarko.
Kuma ta haka ne irin wadannan tsuntsaye na Afirka suke jan hankalin kifayen da inuwar fika-fikansu, inda suke shiga inuwar, kuma hakan ya kai su ga mutuwa.
Inuwar tana ba tsuntsayen damar gani sosai su gano kifin su kamo shi daga cikin ruwa ta hanyar amfani da dogon bakinsu.
“Wannan duk wani bangare ne na dabarun farautar abinci da yake daukar lokaci mai tsawo suna neman abinci,” inji Bill Shields, wanda Farfesa ne a Kwalejin Kimiyyar Muhalli ta SUNY, lokacin da yake bayani ga kafar labarai ta Audubon.