Wani jirgin sama mallakin kamfanin Aero da ya tashi daga Kano da nufin zuwa Legas ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano bayan da wani tsuntsu ya yi masa kaka-gida.
Wani jami’in Hukumar Kashe Gobara a filin jirgin ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na ranar Lahadi.
- Matsalar tsaro na barazana ga kasancewar Najeriya kasa daya – Gwamnonin Arewa
- Yadda ’yan kato-da-gora suka fatattaki ’yan bindiga daga kauyen Abuja
Jami’in, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce jirgin na tsaka da tafiya a sama ne aka gano tsuntsun ya yi masa cikas, lamarin da ya kai ga lalata daya daga cikin injinansa.
“Ka san ba yadda za a yi jirgi ya tafi da inji daya kuma ga fasinjoji a cikinsa.
“Dole jirgin ya dawo ya sauke fasinjojin, bayan an masa gwaje-gwaje kuma ya sake tashi ba tare da fasinjojin ba. Daga bisani kuma an kawo wani jirgin daban wanda ya kwashe su zuwa Legas din,” inji shi.
Kamfanin jirgin na Aero dai a cikin wata sanarwa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya nemi gafarar fasinjojin saboda tsaikon da aka samu.
A cewar sanarwar, “Kamfanin jiragen sama na Aero na neman afuwa kan matsalar da aka samu a jirginmu mai lamba N2 142 a safiyar Lahadi, 21 ga watan Maris 2021 a jirgin da ya tashi daga Kano zuwa Legas saboda kutsen wani tsuntsu.
“Saboda daukar matakan tsaro, kamfaninmu ya tura da jirgin zuwa Legas domin injiniyoyinmu su duba lafiyarsa sannan mu samu amincewar Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) kafin ya dawo ya ci gaba da aiki.
“A lokacin da matukun jirgin ya ji karar tsuntsun a jikin jirgin, sai ya dauki matakin da ya dace na dawowa Kano ya yi saukar gaggawa, duk da cewa dukkan injinansa lafiya kalau suke,” inji kamfanin.