Majalisar Dattawa ta fara aikin kafa hukumar da za ta halasta ta kuma kula da ayyukan masu farauta a fadin Najeriya.
Sanata Biodun Olujimi daga Jihar Ekiti ne ya gabatar da kudurin dokar mai suna: “Kudirin Dokar Mafarauta a Najeriya ta 2020 (SB. 477)”, a zauren Majalisar.
- Kotun Musulunci ta sa a kamo mawaki Rarara kan ‘boye matar aure’
- Fadar Shugaban Kasa ta fara nazarin sake rufe iyakokin Najeriya
- An kara lokacin rajisatar lambar dan kasa da layin waya
- Allah Ne Kadai zai iya tsare iyakokin Najeriya da Nijar
Dokar wadda aka kammala yi wa karatu na biyu za ta kawo karshen rudanin da ake fama da shi game da halascin kungiyoyin mafarauta a Najeriya.
Olujimi ya shaida wa ’yan jarida a ranar Talata cewa yin dokar zai halasta wa mafarauta samar da tsaro a cikin al’umma, tabbatar da bin doka da oda da kuma hidimta wa jama’a.