Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, muna nan dai a kan hanyarmu ta zuwa Aljanna. Muna nan dai a kashi na biyu na tafiyar, wanda ya kunshi ayyuka na kwarai bayan imani, mun kwana a karkashin bayanin yi wa iyaye da’a. Ga ci gaba:
Kada a sake a rika fada musu (iyaye) duk wata magana ko a nuna musu wata alama ta kushe su ko a yi wani abin da zai kaskantar da su ko ta halin kaka! Kada mutum ya yabi kansa cewa ai yana yi musu duk abin da suke bukata, amma dai suna ta sukar abin, ba su nuna godiya. In ma haka ta kasance, wato ba su yabawa, mai yiwuwa ne ba ka kalli yanayin da suke ciki ba ne, har ka lura da irin bukatar da suke da ita ba; domin ko abinci ne, misali, kai abin da kake ganin shi ne mai kyau mai dadi, su ba shi suke bukata ba. Saboda haka lallai ne a lura da irin bukatunsu da kuma lokacin bukatun da yanayinsu.
Sannan duk abin da zai cutar da su kada a yi shi. Duk wata magana ko wani aiki, lallai ne a saurara musu. Koda tafiya ake yi, lallai ne ya kasance shi (mahaifi) ke gaba, kana biye, ba a jerawa ko kuma a gan ka a gaba. In an gan ka a gabansa, to lallai ne ya kasance ka yi haka ne don ka kare masa wani abin da zai cuce shi. Wannan haka abin yake, domin Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda), ya ga wasu mutum biyu suna tafiya tare kuma sun yi kama da juna, sai ya tsayar da su ya ce, “Yaya kuke ne tsakanin junanku?” Sai suka ce masa mahaifi ne da dansa. Sai ya ce, “Shi ne kuke jere? To, ba haka muka koyo ba daga Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mu abin da muka sani shi ne idan mahaifi da dansa suna tafiya, to mahaifin shi ne a gaba, da na biye da shi a baya, sai dai in akwai wata lalura.” Misali idan yana yin magana, ka matso kusa ka rika jin abin da yake fadi, in ya gama ka koma matsayinka a baya. In kun kai wurin da za ku je, to, ba ka zama sai ya zauna; sannan in kun zauna din, to ba ka tashi sai ya tashi.
Sannan lallai ne, kamar yadda ya gabata, kada a yi musu wata magana ta tsawa ko raini, ko wani abin da ba su yarda ba, matukar abin ba sabo ba ne. Kuma ko ma abin ya saba wa Allah, in za a yi musu magana ko a nuna kin abin, ba gatse ko magana mai gautsi za a yi musu ba, magana za a yi musu a hankali da biyayya yadda za su fahimta, su gane. In ba su gane ba, to sai ka tura musu wanda kake ganin in ya yi musu bayani za su gane, wanda suke ganin shi daidai da su ne! Don a wata maganar ba za su saurare ka ba ma, balle su fahimta ko su gane! To, sai ka kyale su a irin wannan yanayi, ka je ka turo musu wani aboki ko wanda suke ganin yana da wata kima a wurinsu don su fahimtar da shi.
2. Zumunta: Sannan kuma sai mu sadar da zumuntarmu, ta fuskar yin da’a gare su da kyautata musu (dangi) da girmama su da ziyartar su da tambayar lafiyarsu da halin da suke ciki, don mu aiwatar da wani abin da zai taimaka musu ta fuskar taya su murnar alherin da suke ciki, ko taya su alhinin wani abin bakin cikin da ya same su. Mu dai yi kokarin gudanar da duk wani abin da zai taimaka wajen karin dankon zumuntarmu da su.
3. Makwabta: Sannan mu kyautata wa makwabtanmu, ta yadda za su ji dadin zamantakewa da mu; mu girmama su, mu kula da sha’aninsu, musamman ma idan suna cikin matsin rayuwa. Sannan mu kare duk abin da zai cutar da su. Duk mai hankali ya kamata ya san abin da zai cutar da waninsa, musamman in aka yi dubi da maganar Hadisin da yake cewa, ka so wa dan uwanka abin da kake so ga kanka, ka ki wa dan uwanka abin da kake ki ga kanka.
4. Bako: Mu girmama shi, mu kyautata masa a kan abin da yake wajibi a kanmu, ta fuska ciyar da shi da ba shi wurin kwana. Lallai mu bayar da hakkokinsa kamar yadda shari’a ta gindaya mana! Wannan babban al’amari ne a cikin guzurin wannan tafiya tamu zuwa Aljanna!
5. Sannan mu girmama dan uwa Musulmi mumini ta fuskar tabbatar da bayar da hakkokin ’yan uwantakar addini da ke tsakaninmu da shi, a kan tafarkin da Musulunci ya dora mu. Hakkokin nan sun hada da yi masa sallama, mun san shi ko ba mu san shi ba, matukar dai shi Musulmi ne shi ke nan! Yana daga cikin alamomin tashin kiyama, Musulmi su ki yin sallama ga ’yan uwansu Musulmi, sai ga wanda suka sani! Sannan mu gaida shi idan ya yi atishawa ya yi hamdala, amma komai matsayinsa, in dai bai yi hamdalar nan ba, to ba za mu gaida shi da kowace irin gaisuwa ba. Akwai bukatar dai a san yadda gaisuwar take da kuma yadda karbawar gaisuwar take a Musulunci.
Sannan yana daga cikin hakkinsa a barrantar (kubutar) da shi a yayin da ya yi rantsuwa, rantsuwar ba zai yi kaza ba, ko zai yi kaza, to kada a matsa masa ya yi din ko ya bari, ta yadda za a sa shi ya yi kaffara, idan ya yi din ko ya ki, matukar dai abin ba sabon Allah ba ne; sannan a gaida shi a lokacin da ba shi da lafiya; sannan a raka gawarsa yayin da ya mutu.
6. Sannan mu yi adalci a cikin zantuttukanmu da ayyukanmu (na yau da kullum) da kuma yayin da za mu yanke wani hukunci. Domin yin adalci a cikin kowane daya daga wadannan abubuwa, lamari ne wanda yake wajibi, wato tilas. Da adalci ne addini da duk al’amuran rayuwa suke tsayuwa ba su lalacewa. Duk lalacewar da ake gani a yau a tsakanin al’umma, rashin adalci ne ya kawo shi. Da an tsayu kan adalci da komai ya tafi daidai kowa ya huta, an zauna lafiya cikin lumana da walwala!
Da adalci ne al’amarin kasa da na al’ummar cikinta yake tsayuwa ya gudana yadda ya kamata! Arziki ya yalwata, zaman lafiya da samu su wadata! Saboda haka lallai a kula da wannan babban al’amari na adalci a rayuwa!
Mu kwana nan.