✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohuwar Shugabar Laberiya ta lashe lambar yabo ta Mo Ibrahim

Kamar yadda masu lura da al’amaru da dama su ka yi hasashe, kallabi tsakanin rawwunar nan, tsohuwar Shugabar Laberiya, Misis Ellen Johnson Sirleaf, ta lashe…

Kamar yadda masu lura da al’amaru da dama su ka yi hasashe, kallabi tsakanin rawwunar nan, tsohuwar Shugabar Laberiya, Misis Ellen Johnson Sirleaf, ta lashe lambar yabo ta Mo Ibrahim dan asalin kasar Sudan da ke zaune a Amurka kan shugbanci nagari a Afirka. Wannan lambar yabo tana hade da kyautar Dalar Amurka miliyan biyar.

Ita dai wannan kyautar lambar yabo ta Mo Ibrahim lamba ce da ke yaba wa shugabanni da suka nuna kwarewa da kyautatawa a shugabancinsu a yankin Afirka kamar yadda Muryar Amurka ya ruwaito.

Ita dai Ellen ta kammala wa’adin mulkinta a watan jiya, inda kuma shi ne canjin mulkin dimokuradiyya na farko a tarihin Laberiya tun  1944. 

Haka kuma Sirleaf ta samu lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya, kuma ita ce mace ta farko da ta taba zama Shugabar kasa a Afirka kuma har ta yi wa’adi biyu, kowanne na tsawon shekara 6 ta sauka bana bayan an sake zabe domin kundin tsarin mulkin kasar bai ba ta damar sake tsayawa takara ba.

Dokta Salim Ahmed Salim, Shugaban Kwamitin Bayar da Kyauta ta Mo Ibrahim ya fada a lokacin da yake bayyana kyautar cewa Ellen ta karbi shugabanci a Laberiya a lokacin da Yakin Basasa ya gama ragargaza kasar, kuma ta yi kokarin kawo zaman lafiya da gina kasar da kuma cibiyoyin dimokuradiyya. Ya ce duk da nasarar da aka samu tilas a samu wasu kura-kurai, amma duk da haka Sirleaf ta aza tubalin da yanzu za a iya ci gaba gina Laberiya a kai.

Tsohuwar jakadiyar Amurka a Laberiya, Linda Thomas- Greenfield ta ce Ellen ta bar kasar a yanayin da ya fi hali da ta sau Laberiya a ciki, ta kuma kara da cewa akwai sauran jan aiki a gaba.