✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohuwar matar shugaban APC ta fito takarar Gwamnan Nasarawa

Tsohuwar matar Sanata Abdullahi Adamu ta sha alwashin kawo sauyi idan aka ba ta dama.

Dokta Fatima Abdullahi, tsohuwar matar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ta sayi fom din takarar Gwamnan Jihar Nasarawa, don karawa da gwamna mai ci, Abdullahi Sule, a zaben 2023.

Dokta Fatima za ta gwada kwanjinta a zaben fidda-gwani da APC za ta gudanar a Jihar a wannan wata da muke ciki.

Cikin wata tattaunawa da Aminiya a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa ranar Asabar, Dokta Fatima ta ce ta sayi fom din ne don ta shiga goga da ita sannan ta yaki rashin iya shugabanci a jihar.

“Jihar Nasarawa na bukatar shugaba mai hangen nesa, wanda ya san me ya ke yi sannan zai iya tsayawa tsayin-daka wajen ciyar da jihar nan gaba.

“Abin da ya karfafa min guiwa shi ne halin da jiharmu ke ciki saboda muna bukatar mutumin da zai inganta tattalin arzikin jihar, sannan ya tabbatar da ci gaban da iyayenmu suka dasa, kuma ni ce wadda za ta iya samar da wadannan canji.

“Na dade ina ganin yadda abubuwa suke tafiya a jihar nan, amma wannan lokaci ne da ya kamata na fito a dama da ni na kuma bayar sa tawa gudumawar,” a cewar Dokta Fatima.

Ta ce matasa na mutuwa cikin talauci saboda ba a samar musu da ingantacciyar rayuwa ba, amma da zarar an zabe ta, za ta zabi mutane masu hazaka da za su yi aiki wajen tafiyar da gwamnati yadda ya kamata.

“Don haka, na zo nan ne in roke ku, ku taimaki muradina na son zama gwamna ta hanyar zaba ta a matsayin ’yar takarar zaben gwamna a 2023.