✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohuwa ta babbake danta da iyalansa

Ana zargin wata tsohuwa mai shekaru 75 ta cinna wa danta, jikokinta biyu da kuma surukarta wuta a Jihar Ondo.

Ana zargin wata tsohuwa mai shekaru 75 ta cinna wa danta, jikokinta biyu da kuma surukarta wuta a Jihar Ondo.

Ana zargin dattijuwar ta yi ajalin dan nata da iyalansa ne bayan ta watsa musu fetur sannan ta cinna musu wuta a cikin gidansu, lamarin da ya haddasa mummunar gobara.

Aminiya ta ruwaito cewa abin ya faru ne a wani kauye da mai suna Aponmu da ke wajen garin Akure, babban birnin jihar.

Majiyarmu ta shaida mana a ranar Talata cewa an kai magidancin da iyalan nasa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Owo, inda likitoci suka tabbatar cewa shi da matarsa da daya daga cikin yaran sun rasu.

“Babban dan ne kadai ya rayu, shi ma din a yanzu haka yana cikin mawuyacin hali,” in ji shaidar.