Allah Ya yi wa tsohon shugaban kamfanin NNPC Maikanti Kachalla Baru rasuwa.
Maikanti Baru ya rasun ne a daren Juma’a kamar yadda shugaban NNPC na yanzu Mele Kyari ya sanar da safiyar nan.
“Dan uwana, aboki kuma shugaba, Dr Maikanti Kachalla Baru, tsohon shugaban NNPC ya rasu a daren jiya.
“Ya kasance mutum ne mai kyawawan dabi’u abin koyi. Allah Ya yi masa rahama,” inji shi.
My brother, my friend and my mentor, Dr Maikanti Kachalla Baru, immediate past GMD of NNPC died late last night. He was of exemplary character and disposition. May Allah forgive him and have mercy upon him.
— Mele Kyari, OFR (@MKKyari) May 30, 2020
Marigayin shi ne shugaban NNPC daga 2016 zuwa watan Yulin 2019 kafin ya mika ragamar kamfanin ga Mele Kyari mai ci a yanzu.
Muhimman abubuwa game da Maikanti Baru.
An haifi marigayi Maikanti Kachalla Baru a watan Yulin shekarar 1959. Ya rayu shekara 61 a duniya.
Marigayin dan asalin Karamar Hukumar Jama’are ne jihar Bauchi a Arewa maso gabashin Najeriya.
Ya taso a yankin Arewa ta tsakiya a garin Jos na jihar Filato mai makwabtaka da Jiharsa ta asali. A nan ya yi karatunsa na firamare da sakandare wanda ya kammala a 1978.
- Tsohon Shugaban NNPC Maikanti Baru ya rasu
- Kisan Alex Badeh: Kotu ta yanke wa sojoji 6 hukuncin dauri
- ‘Yan bindiga: Gwamnonin Arewa za su yi taron dangi
A 1983 ya kammala dagirinsa na farko da daraja ta daya a bangaren injiniya a fannin injuna daga Jami’ar Ahmadu Bello.
Ya samu digirin digirgi a da Jami’ar Sussex ta kasar Birtaniya a Fannin Aikin Injiya da Taimakon Na’ura.
Kwarewa da aiki
Shi babban mamba ne a Kungiyar Injiniyoyi ta Najeria (NSE). Yana na matukar kima a idon takwarorinsa.
Ya zama Darektan kamfanin Carlson Services mallakar NNPC a kasar Birtaniya daga watan Dismaban 2007 zuwa Janairun 2007.
An nada shi shugaban kamfanin NNPC na 18 a 2016. Ya rike kujerar har lokacin ritayarsa bayan cikarsa shekaru 60 a watan Yulin 2019.
Kafin nan shi ne Mai Ba tsohon Karamin Ministan Mai Shawara na Musamman Kan Albarkatun Mai na Kan Tudu.
Gabanin haka an nada shi Babban Darektan Rukunin NNPC Kan Bincike da Hako Mai.
Mukamin da ya rike kafin wannan shi ne Babban Manaja NNPC kan Sarrafa Iskar Gas.
Ya kuma taba zama Babban Manajan Rukuni na Lura da Albarkatu da Zuba Jari.
Shi ne kuma tsohon Mai Sasanci na NNPC kan Aikin Shimfida Bututun Iskar Gas na Yammacin Afirka daga 1999 zuwa 2004.
A ranar 30 ga watan Mayu 2020 ne aka sanar da rasuwan tsohon shugaban na NNCP Maikanti Baru.