Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa Malam Adamu Ahmed Sarawa, wanda aka fi sani da ‘Saboda Stamps’ ya rasu.
Marigayin ya rasu yana da shekara 66 bayan gajeriyar rashin lafiya a gidansa da ke Kano.
Kafin rasuwarsa ya taba zama Dan Majalissa mai wakiltar karamar hukumar Kafin Hausa har sau biyu daga shekarar 2007 zuwa 2015 a karkashin inuwar jam’iyar PDP a zamanin gwamnatin Alhaji Sule Lamido.
Kana shi ne shugaban majalisar dokokin da ya fi ko wanne dadewa a kan karaga da ba a taba tunanin tsigewa ba, tun daga lokacin da aka kirkiri jihar Jigawa a shekarar 1991.
An haifi marigayi Ahmed Sarawa, a kauyen Gurgun Daho da ke kusa da gundumar Sarawa a cikin karamar hukumar Kafin Hausa a yankin masarautar Hadejia da ke Arewa maso Gabas a jihar Jigawa.
Shi dai malamin makaranta ne kafin daga baya marigayi Malam Ibrahim Shehu Kwatalo ya sanya shi cikin harkokin siyasa.
Ya taba zama shugaban karamar hukumar Kafin Hausa ya kuma rike shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Jigawa a lokacin mulkin tsohon gwamnan Jigawa Saminu Turaki a karkashin jam’iyar ANPP.
A wannan lokacin ne ya taba zama Amiril Hajj ya kuma jagoranci tawagar alhazan jihar Jigawa zuwa kasa mai tsarki na tsawon wasu shekaru.
Marigayi Ahmad Sarawa, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya, an kuma yi masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.