Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ƙaryata zargin da ake masa cewa shi ne ya ƙaƙaba ɗan cikinsa, Mustapha, a takarar Gwamnan Jihar a zaben 2023.
A cewar Sule, wanda ƙusa ne a jam’iyyar ta PDP a Najeriya, ba shi da masaniyar yadda aka yi har ɗan nasa ya tsaya takara ya lashe zaɓen, inda ya ce shi ma a dandalin sada zumunta na Facebook ya ga labarin a lokacin.
- Yadda ‘yan kasashen waje ke zuwa koyon Harshen Hausa a Jami’ar Bayero
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 99, sun kuɓutar da mutum 139 a mako guda
Ya bayyana haka ne a cikin wata tattaunawarsa da Daily Trust a ranar Lahadi.
Tsohon Ministan na Harkokin Waje ya kuma ce, “Abin takaici ne yadda siyasar Afirka da ta Najeriya ta koma yadda mutum zai riƙa yin kowacce irin ƙarya don kawai ya ci zaɓe. Shi ya sa na ce ya kamata a ce akwai iyakar abin da mutum zai iya yi da wanda ba zai iya ba.
“Game da batun ɗana (Mustapha), Wallahi ban san yadda aka yi ya zama ɗan takarar [Gwamnan Jigawa] ba. Wallahi PDP ba ta faɗa min ba, ni ma a Facebook na gani.
“Amma yanzu mutane na cewa na ƙaƙaba ɗana, shi ya sa muka faɗi, ba haka ba ne? Shi ya sa ba ni da mafita, sai zagi na ake yi. Mutane duk sun manta da gudunmawar da na bayar a Najeriya tun a 1979 da na zama ɗan Majalisar Wakilai, da ma irin tsangwamar da na sha a ta yadda hatta shugaban kasa na jam’iyyata (Jonathan) sai da ya sa aka gurfanar da ni a gaban kotu da ’ya’yana kan zargin sata.
“Ni fa. Ni da nake a matsayin uba a PDP kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙirƙire ta, amma Shugaban Kasa ɗan jam’iyyata ya ga dole sai ya ɓata min suna kafin buƙatarsa ta siyasa ta biya,” in ji Sule Lamido.
Sai dai da aka tambaye shi ko zai kuma tsayawa takarar Shugaban Kasa a zaben 2027 mai zuwa, ya ce, “Ni na tsufa ai, shekara ta 75 yanzu. Na haƙura na bar wa matasa irin ku.”
A kan kamun ludayin gwamnatin APC ta Shugaba Bola Tinubu kuwa, tsohon Gwamnan na Jigawa ya ce ’yan Najeriya ne suke ɗanɗana kuɗarsu tun da su suka ce PDP ta ba iya ba.