Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule lamido ya ce, gwamnonin arewacin Najeriya da suka tafi Amurka taro sun tallata rashin sanin kundin tsarin mulkin ƙasarsu.
Gwamnonin Arewa sun tafi Amurka halartar taron zaman lafiya da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta shirya.
Sule Lamido a wani rubuta da ya wallafa a Facebook ya ce, alhakin tsare rayuka da dukiyar ‘yan ƙasa ya rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya ne, kuma hakan yana nan a fayyace cikin jerin ayyukan ɓangaren zartarwar.
Rubutun da ya yiwa taken, “‘Kun Je Kun Kunce Mana Zane A Kasuwa!’ domin samun mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaron da ke addabar yankinku, kun kai kuka gidan mutuwa.
- NAJERIYA A YAU: Wane Cigaban Tsaro Za A Samu Bayan Taron Gwamnoni A Amurka?
- Yadda Wahalar Man Fetur Ta Yi Tsanani A Najeriya
“Yadda suka bayyana damuwarsu da matsalolin tsaro abin yabawa ne, amma tafiyar da suka yi zuwa Amurka ya ƙara bayyana cewa ba su fahimci Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ba.
“Ba su fahimci ainihin makamin da ya ba su ikon zama gwamnoni ba. Sun jahilci wannan kundi.
“Idan da gwamnonin sun yi tafiyar ne don domin laluben yadda za a bunkasa noma ko al’amurran kiwon lafiya ko wasu matsaloli masu rangwamen muhimmanci na cikin gida to wannan babu laifi.
“Amma tafiya domin tattaunawa a kan abin da kundin tsarin mulkinmu ya ce alhakin bangaren zartarwa ne, gaskiya wannan bayyana rashin sanin cikakken abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ƙunsa ne.
“Da sun zauna a gida sun je cibiyoyinmu masu albarka kamar NIPSS a Kuru Jos ko ASCON a Badagry.
“Wadannan cibiyoyi na da isassun kayan aiki da ƙasidu da samfuran matsaloli da mafita kan tsaro a Najeriya fiye da Cibiyar Nazarin da suka tafi a Amurka”.
Hotuna da bidiyon gwamnonin da suka yi wannan tafiya a kafafen sada zumunta na cigaba da shan mabambanta ra’ayi.
Wasu na cewa an je kashe kuɗin talakawa ne wasu kuma na yabawa.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu irin wannan tafiya da nufin halartar taron tattaunawa kan matsalar tsaro musamman a Arewa Maso Yammacin Najeriya.