✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na ɓoye wa ’yan Najeriya gaskiyar halin da ƙasa ke ciki — Sule Lamido

Tsohon gwamnan ya ce jam'iyyar APC ta zame wa 'yan Najeriya annoba.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin bayyana wa ‘yan Najeriya gaskiyar halin da ƙasar nan ke ciki.

Da yake magana a shirin ‘Gane Mini Hanya’ na BBC Hausa.

Lamido, wanda ke cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP, ya kuma caccaki tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa rashin bayyana gaskiya lokacin mulkinsa.

“Gwamnatin Buhari da Tinubu ba sa bayyana wa ’yan Najeriya gaskiya, ba kamar lokacin da PDP ke mulki ba, inda komai ya kasance a fili ga kowa.

“Amma da zuwan Buhari, ya fara amfani da yaudara da ƙage wajen tafiyar da mulki,” in ji shi.

Lamido ya kuma yi tambaya kan matakin Shugaba Tinubu na ciwo bashi, inda ya bayyana cewa abin da gwamnati ke faɗa wa ’yan Najeriya ya saɓa wa abin da ta ke yi.

“Idan har ’yan Najeriya za a faɗa wa gaskiya, babu matsala. Amma yaya za ka tsara kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 30, ka tara Naira tiriliyan 50, amma har yanzu kake neman ciwo bashi alhali kana da ribar Naira tiriliyan 20?” in ji shi.

Ya kuma soki gwamnatin mai ci kan abin da ya kira rashin sanin ya kamata da son zuciya.

“Irin wannan rashin hankali ba a yi a ko ina a duniya. Amma sai ga wasu ‘yan Najeriya suna goyon baya.

“Ka duba kafafen sada zumunta, ana cewa APC annoba ce, amma har yanzu akwai masu kare ta.”