Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina a kama wani tsohon Shugaban Karamar Hukumar Jibiya bisa zargin taimaka wa ’yan bindiga a Jihar.
An dai cafke Haruna Musa Mota ne bisa zargin taimaka wa da kuma daukar nauyin ’yan bindiga da masu garkuwar da suka addabi sassan Jihar.
- Yadda Rikadawa ya martaba yaronsa da auren ’yar cikinsa
- Kwamandan ’yan bindiga Daudawa ya mika wuya a Zamfara
A wani sakon murya da ya karade kafafen sa da zumunta na zamani a karshen makon da ya gabata, an zargi Haruna Mota da tattaunawa da daya daga cikin wadanda suka sace daliban makarantar Sakandiren Kankara a kwanakin baya.
Da yake tabbatar da kamen ranar Litinin, Kakakin Rundunar, SP Gambo Isah ya ce tuni aka gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, kuma yanzu haka yana nan a tsare a gidan yari.
“Gaskiya ne mun gurfanar da shi kuma zarge-zargen da ake masa sun hada da hadin baki, taimaka wa ’yan bindiga, ’yan fashi, masu garkuwa da kuma ta’addanci,” inji kakakin.
A baya dai Gwamnatin Jihar Katsina ta sha zargin cewar ana yi wa yakin da yake yi da bata-garin zagon kasa ta hanyar tallafa musu da bayanai da kuma kudade.