✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon shugaban Kamfanin Konga ya kashe kansa a Legas

Kafin rasuwarsa, ya yi wa wani ɗan uwansa da ke Amurka bayanin yadda zai raba dukiyarsa.

Tsohon Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Konga mai hada-hada ta intanet, Nick Imudia ya kashe kansa a Jihar Legas.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan ba tare da wani ƙarin bayani ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, Imudia wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Ika ta Kudu a Jihar Delta, ya faɗo ƙasa daga barandar benen gidansa da ke Lekki a Legas a Yammacin ranar Talata.

A cewar kafar yaɗa labarai ta yanar gizo TheWill, kafin rasuwarsa, ɗan kasuwar ya kira wani ɗan uwansa da ke zaune a Amurka, domin ya ba shi bayanin yadda zai raba dukiyarsa.

Kazalika, ya kira ‘yarsa ƙarama yana sanar da ita cewa kar ta shiga damuwa domin zai kasance tare da ita.

Makusanta da dangi da abokan hulɗar Imudia sun shiga cikin alhini da baƙin cikin yanayin da ya ɗauki ransa.

Rahotanni sun bayyana cewa ya auri mahaifiyar ‘yarsa ƙarama amma auren ya mutu sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakaninsu.

Daga bisani ya sake shiga daga ciki inda ya auri wata Ba’amurkiya.