✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Kaduna ya rasu

Tsohon shuagaban ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, Ibrahim Yaro Suleiman ya rasu, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Jam’iyyar PDP, a cikin sakon ta’aziyyar da Sakataren Yada Labaran Jihar, Abraham Alberah Catoh, ya fitar, ya jajanta wa ’yan uwan mamacin.

Ya ce Shugaban jam’iyyar na jihar, Felix Hassan Hyat da daukacin Kwamitin Zartaswa na Jiha, suna mika ta’aziyyarsu ga iyalan Ibrahim Yaro Suleiman.

A cewar sanarwar, marigayi Ibrahim Yaro Suleiman ya kasance hazikin dan siyasa kuma dattijo mai kima.

Daga nan kuma ya yaba da irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban jam’iyyar a jihar lokacin da yake raye, inda ya ce ba za a taba mantawa da shi ba.

Jam’iyyar ta kuma mika ta’aziyyarta ga abokansa da masoyansa, tare da yi wa ’yan uwa addu’ar Allah Ya jikan sa da gafara.