✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban China, Jiang Zemin, ya rasu

Jiang ya rasu ne a Shanghai ranar Laraba, inda ya  bar duniya yana da shekara 96.

Rahotanni daga kasar China sun ce tsohon Shugaban Kasar, Jiang Zemin, ya rasu.

Jiang ya rasu ne a Shanghai ranar Laraba, inda ya  bar duniya yana da shekara 96.

Sanarwar rasuwar marigayin na kunshe ne cikin wata wasikar hadin gwiwa tsakanin hukumomin kasar da kuma babbar jam’iyyar kasar suka fitar.

Wasikar ta nuna yadda dukkan wadanda wasikar ta shafa suka mika ta’aziyyarsu ga al’ummar China dangane da rasuwar tsohon Shugaban.

Kazalika, wasikar ta nuna marigayin a halin rayuwarsa, shugaba ne tsayayye kuma mai kima a idon duniya wanda ya kasance abin so ga daukacin al’ummar kasar.

Ta kuma bayyana matuwarsa a matsayin babban rashi ga kasar baki daya.

(NAN)