✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon shugaban majalisar Edo ya rasu

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo Zakawanu Garuba, ya rasu. Zakawanu Garuba wanda ya yi wa’adi biyu a Majalisar ya rasu…

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo Zakawanu Garuba, ya rasu.

Zakawanu Garuba wanda ya yi wa’adi biyu a Majalisar ya rasu ne a ranar Asabar sakamakon rashin lafiya a wani asibiti a Abuja.

Marigayin ya fara zuwa majalisar ne a shekarar 2003 a karkashin inuwa jam’iyyar PDP kafin daga bayan ya zama shugaban Majalisar a 2007.

An haife shi a ranar 23 ga Agusta 1965 a kauyan Akpekpe da ke Masarautar Auchi a Karamar Hukumar Etsafko ta Yamma a jihar ta Edo.